Botanix – Mujalla akan shuke-shuke

Botanix Hausa

Welwitschia mirabilis – noman matacciyar shuka mai rai

picture

Welwitschia (Welwitschia mirabilis) tsahuwar shuka ce mai fitowa a gefen kogin Atlantika a Qasar Namibiya Kudancin Angola. Welwitschia a haqiqa bashiya ce, duk da cewa a fisge ba ta kama da bishiya. Gaba xayan shukar tana da gangar jiki guda xaya wanda ganye biyu ke fita – wannan yana kama da tsakiya wadda gefunanta bai haxu ba. Welwitschia wani lokaci tana kama da tarin shara!

Lahadi 24.12.2023 07:45 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare

Bishiyar Taba (Nicotiana glauca) – bishiyar kan baranda abar hange daga nesa!

picture

Bishiyar Taba (Nicotiana glauca)

Buqatar xan adam ta sabon abu, mai ban mamaki da abin da yake ba-saban-ba taqaitacce ne. Sabo da haka, manoman lambu ke mafarkin wani abu sabo a lambunsu – wani abu wanda ba kowa ya ke da shi ba. Da wannan dalili Kasuwar shuke-shuke ke bawa manoma wani abu sabo a duk shekara – domin kwantar da qishirwar da manoma ke da ita wajen samun abu na asali. Gabatar da sababbin ire-ire zai sanya shukar bishiyar taba ta shiga duk hannun manoma ba da daxewa ba.

Lahadi 24.12.2023 07:42 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare

Qwara mai jure rava Rhapidophyllum hystrix (Qwara Mai Allura)

picture

Rhapidophyllum hystrix

Rhapidophyllum hystrix xaya ce daga ire-iren qwara mai jure rava. Akwai nau’i qwaya xaya na wannan shuka Rhapidophyllum. Wurin da wannan shuka tafi fitowa shine Kudu maso Gabacin Amurka. To amma, godiya ga juriyarta wadda ya kai qasa da 20 °C shuka ce sananniya a duniya, musamman a Turai.

Lahadi 24.12.2023 07:39 | buga | Kwakwa

Noman Mangwaro daga tsaba

Ka shuka sabuwar tsaba domin samun kyakkyawar tsirowa. Ka jiqa tsabar a ruwa mai ximin kimanin 20–25 °C zuwa kimanin awa 2–6.

Lahadi 24.12.2023 07:34 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare, Dokoki akan noman shuke-shuke

Mangwaron Kalimantan, Kasturi (Mangifera casturi)

Mangwaron Kalimantan (Mangifera casturi) wanda a gargajiyance aka fi sani da Kasturi bishiya ce da ake samu a wurare ‘yan qalilan mai tsawon kimanin mita 10–30 mai fita a qasashe masu zafi a zagayen Banjarmasin a kudancin Borneo (Indonisiya). A halin yanzu babu bishiyar a daji sabo da haramtattun masu saran bishiya. To amma, a wasu lokutan ana noma ta a waxannan wurare sabo da ‘ya’yanta da ke da daxi.

Lahadi 24.12.2023 07:32 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare

Continue: 1-5 6-10 11-15 16-20 21-22

Dangane da KPR

Logo of KPR - Qungiyar Manoman Lambu ta Slovakiya
KPR - Qungiyar manoman lambu qungiya ce ta qasa-da-qasa. Qara karatu...
Yi musayar ra'ayinka dangane da noman shuke-shuke. Rubuta batu akan lambu, shuke-shuke, noman shuke-shuke da sauransu kuma ka buga shi a yarenka a mujallarmu ta Botanix! Ka tuntuvemu domin qarin bayani.

Category: Duk Bado Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya Ciyawa Dokoki akan noman shuke-shuke Kwakwa Qwari Shuke-shuken qasashen qetare Shuke-shuken ruwa