Botanix – Mujalla akan shuke-shuke

Botanix Hausa

Bishiyar Khasi Pine (Pinus kesiya)

Bishiyar Khasi Pine (Pinus kesiya) iri ne mai saurin fitowa daga Asiya, wadda ba’a nomata a wani wuri daban. Bishiyarta kan kai tsawon kimanin mita 30–35 da kuma kaurin gangar jiki mai murabba’in mita 1. Ko wane reshe na da vangarori uku – ko wane xaya kimanin tsawon santimita 15 zuwa 20. ‘Ya’yan itacen wannan bishiya (cones) suna kaiwa tsawon kimanin santimita 5 zuwa 9 kuma tsawon tsabar ya kai kimanin santimita 1,5 zuwa 2,5.

Asabar 23.12.2023 20:45 | buga | Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya

Shuka fulawa mai siffar qwai da yabanya

Fitar da fulawa mai siffar qwai da yabanya wadda ka karva daga cikin maqunshinta ta hanyar saqon waya, kuma ka barta a inuwa har zuwa wasu kwanaki 2–3. Ta wani vangaren kana iya shuka su nan take kuma ka ajiye su a inuwa zuwa wasu kwanaki ta yadda zafin rana ba zai tava su kai tsaye ba.

Asabar 23.12.2023 20:41 | buga | Dokoki akan noman shuke-shuke

Burodin xan itace Artocarpus odoratissimus, Marang

Genus Burodin xan itace (Artocarpus) bishiya ce da ta qunshi kimanin ire-ire 60 na bishiyoyin yanayin qasashe masu zafi dangin Moraceae (dangin bishiyar da aka fi sani da mulberry ko kuma fig). Ana samun su a Kudu maso gabas na Asiya da kuma tsibiran Tekun Pacific. Burodin xan itace na da dangantaka da Ficus (fig trees). Bishiyar Burodin xan itace da aka fi nomawa ita ce Artocarpus altilis. Yawancin sauran ire-iren kamar Artocarpus communis, Artocarpus integer (Cempedak), Artocarpus heterophyllus (Jackfruit, Nangka) kuma Artocarpus odoratissimus (Marang) su ma vangare ne na dangin Burodin xan itace.

Asabar 23.12.2023 20:29 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare

Yaya za ka yi maganin qwaron wake?

Ina zato ba sai na gabatar maka da qwaron wake ba. Wannan wani qaramin qwaro ne girmansa milimita 3–4, da ake samu a tsaba a cikin xakin girki ga misali.

Wannan maxarnacin qwaro yana haifuwa a duk tsaba mai kwanso. A gaskiyance, duk wata tsaba mai kwanso na da wasu daga cikin wannan halitta – gujiya – qwaron gujiya (qwaro), jinvirin wake – qwaron jinvirin wake, lentils – qwaron lentils, waken lambu – kwaron waken lambu da sauransu.

Asabar 23.12.2023 20:20 | buga | Qwari

NOVODOR FC domin yaqi da qwarin dankalin Kwalarado

Ba na zato sai na gabatar da qwaron dankalin Kwalarado (Leptinotarsa decemlineata) domin kowa ya san wannan babban qwaro mai lalata dankali kuma wanda yake da wahalar kashewa ba tare da sinadarai ba. A wani lokaci, babu wanda ya san yadda za’a yi maganin wannan qwaro na dankalin Kwalarado.

Asabar 23.12.2023 20:18 | buga | Qwari

Noman ciyawar kifi (Pleurotus ostreatus)

Ciyawar kifi (Pleurotus ostreatus) sananniya ce a ‘yan kwanakinnan fiye da ciyawa game-gari (ciyawar champignon)! Dangantaka da ciyawa game-gari, Ciyawar kifi ta na da wata rana guda xaya – ba ta rikicewa da ciyawa mai guba “hular mutuwa” (Amanita phalloides).

Asabar 23.12.2023 19:42 | buga | Bado

Cherimoya (Annona cherimola)

Abin sha’awa a halin yanzu ana shigo da kayayyakin marmari na qasashe masu zafi zuwa Turai. Na sami nasarar sayen xan itacen cherimoya kuma na xanxana shi. Ba’a samun sa a shaguna to amma godiya ga xanxanawar da nayi, nan gaba za’a sami wannan xan itace a shago!

Asabar 23.12.2023 19:30 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare

Kiwano (Cucumis metuliferus)

Kiwano xan itace mai kama da lemon zaqi na da tsawon santimita 10–15. Yana cikin dangin gurji. ‘Ya’yan itatuwan na da zankwaye a vawonsu yadda zai tunawa mutum yanayin kayan yaqi irin na mutanen da. Tsakiyar xan itacen kore ne kuma na da ‘ya’ya a cikinsa masu tsawon milimita 5–10. Lokacin da bai nuna ba xan icen kore ne.

Asabar 23.12.2023 19:20 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare

Yaya za kayi da nomammiyar ciyawa?

Idan kana buqatar kyakkyawa, ciyawar da aka aske, sai akai-akai kana nome shingenka. Saurara kaxan, ciyawar da aka nome kan bayar da ciyawa mai yawa wanda wannan matsala ne gareka. Mafi yawan manoman da na sani kan yi maganin ciyawarsu daga sharar gidansu. Sai kawai in girgiza kaina cikin mamakin yadda ake asarar taki mai sauqi!

Asabar 23.12.2023 19:09 | buga | Ciyawa

Ta yaya za ka nome lambunka dai dai?

Ya zama wajibi ka san yadda za ka nome lambunka dai dai domin samun ciyawa mai kyau. Babu bishiya mai yanayin qwai da zata yi kyau idan lambu ba shi da kyau!

Asabar 23.12.2023 19:07 | buga | Ciyawa

Shuke sabon shinge

A Turai lokacin da yafi dacewa da shuke sabon shinge ko kuma shuka qarin ciyawa a shingen da ake da shi ya fara daga watan Mayu zuwa Yuni. Idan aka sami qarancin ruwan sama da marka, watan Yuli na iya zama lokaci mafi dacewa.

Asabar 23.12.2023 18:01 | buga | Ciyawa

Kwakwar tsaunin Boliviya (Parajubaea torallyi)

Parajubaea torallyi kyakkyawar kwakwa ce daga Kudancin Amurka. To amma, ba safai manoma ke noma ta a wajen wurinta na ainihi ba, Boliviya, sabo da girman tsabarta (wannan yana nufin tsadar sufuri)

‘Yar ainihin Boliviya, tana fitowa a wuri busasshe, kuma mai qura, a zazar inter-Andea a wuri mai mita 2700–3400 a sama da kogi. Sabo da haka, kwakwar ita ce irin kwakwa mai fita a wannan yanayi a duk duniya. Yanayin zafi da wahala ya kai sama da 20 °C kuma ravar dare kan zuba babu qaqqautawa. Wasu lokuta yanayin sanyin wurin kanyi qasa da –7 °C a lokacin watannin hunturu (Yuli da Agusta) kuma ruwan sama milimita 550 ne kawai.

Asabar 23.12.2023 17:53 | buga | Kwakwa

Continue: 1-22

Dangane da KPR

Logo of KPR - Qungiyar Manoman Lambu ta Slovakiya
KPR - Qungiyar manoman lambu qungiya ce ta qasa-da-qasa. Qara karatu...
Yi musayar ra'ayinka dangane da noman shuke-shuke. Rubuta batu akan lambu, shuke-shuke, noman shuke-shuke da sauransu kuma ka buga shi a yarenka a mujallarmu ta Botanix! Ka tuntuvemu domin qarin bayani.

Category: Duk Bado Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya Ciyawa Dokoki akan noman shuke-shuke Kwakwa Qwari Shuke-shuken qasashen qetare Shuke-shuken ruwa