Botanix – Mujalla akan shuke-shuke

Botanix Hausa

Noman Mangwaro daga tsaba

Ka shuka sabuwar tsaba domin samun kyakkyawar tsirowa. Ka jiqa tsabar a ruwa mai ximin kimanin 20–25 °C zuwa kimanin awa 2–6.

picture

Wankakken irin Mangwaron Kalimantan, Kasturi (Mangifera casturi), Borneo, Indonesia

Bayan jiqawa, shuka irin a qasa (marar nauyi, mai rairayi) kuma ya kasance ximin tukunyar ya kai a qalla 20–25 °C. Tsaba za ta fito a cikin makwanni 1–3. A ajiye jaririyar shuka a waje mai sauqin zafin rana.

picture

Tsirar tsabar Mangwaron Kalimantan, Kasturi (Mangifera casturi), Borneo, Indonesia

Idan kana zaune a qasashe masu zafi, za ka iya shuka bishiyar Mangwaron a lambunka. Idan kana zaune a qasar da ke da sanyi ko rava, ya zama wajibi ka adana shukar Mangwaron a cikin gida ka kuma a xaki na musamman.

««« Batun baya: Mangwaron Kalimantan, Kasturi (Mangifera casturi) Batun gaba: Qwara mai jure rava Rhapidophyllum hystrix (Qwara Mai Allura) »»»

Lahadi 24.12.2023 07:34 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare, Dokoki akan noman shuke-shuke

Dangane da KPR

Logo of KPR - Qungiyar Manoman Lambu ta Slovakiya
KPR - Qungiyar manoman lambu qungiya ce ta qasa-da-qasa. Qara karatu...
Yi musayar ra'ayinka dangane da noman shuke-shuke. Rubuta batu akan lambu, shuke-shuke, noman shuke-shuke da sauransu kuma ka buga shi a yarenka a mujallarmu ta Botanix! Ka tuntuvemu domin qarin bayani.

Category: Duk Bado Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya Ciyawa Dokoki akan noman shuke-shuke Kwakwa Qwari Shuke-shuken qasashen qetare Shuke-shuken ruwa