Shuke sabon shinge

A Turai lokacin da yafi dacewa da shuke sabon shinge ko kuma shuka qarin ciyawa a shingen da ake da shi ya fara daga watan Mayu zuwa Yuni. Idan aka sami qarancin ruwan sama da marka, watan Yuli na iya zama lokaci mafi dacewa.

Shuke sabon shinge

Wurin da ya kamata ka shuka sabon shingenka ya zama ya kai zurfin santimita 10–15. Sannan sai ka daidaita zurfin da qasar ciko.

Yanzu kana da dama guda biyu:

a) Shuka ‘ya’yan ciyawa

Da farko, sai ka auna wurinda ka ke so ka yi shukar. Sannan sai ka qiyasta nawa ne irin da ka ke da buqata. Ka sani cewa kana buqatar giram 25 na tsaba a duk faxin da ya kai murabba’in mita 1. Bugu-da-qari, kana buqatar qarin giram 25 a duk murabba’in mita 10. Bayan haka, ka tabbatar tsabarka sabuwa ce a lokacin da ka ke sayenta domin irin ciyawa na rasa kuzarinsa na fitowa idan ya daxe. ( Duk irin da ya kai shekara biyu yana rasa kuzarinsa na fitowa da 50%).Kuma ka lura da yadda aka adana tsabar a shago (idan tsabar ta jiqe, ko kuma tuni har sun fara tsiro, ya fi kyau kada ka sayi tsabar – ta haka za ka kaucewa da-na-sani). Akwai banbanci wajen farashin tsabar ciyawa daga Yuro 3 ko wane kilogiram (ya danganta da yanayinsa).

Ka zavi irinka akan yanayin shingen da ka ke da buqata (kana so ka dinga tafiya a kansa kawai, gudu a kansa, yin amfani da shi domin motsa jiki, ko kuma domin amfanin dabbobi). ‘Yan kasuwa na ainihi kan wallafa qananan littatafan bayanai domin taimaka maka wajen zaven iri daga cikin irirruka daban daban domin zaven wanda ya dace da buqatarka. Manyan shagunan sayar da kaya kan bayar da waxannan littatafai idan an nema. Ka da ka sayi iri ba tare da samun bayani akan buqatarka ba.

Ka adana tsaba a wuri marar zafi, basasshe, bayan ka saya. Muna baka shawara kada ka ajiye tsabar ta wuce shekara guda domin tana rasa kuzarinta na fitowa. Ka yi shuka a Mayu ko Yuni. Kafin shuka, yi amfani da manjagara ka yi xan rami mai zurfin santimita 1 a cikin qasa. Bayan shuka, ka mayar da qasar (da matunkuxin qasa ga misali) sannan ka yi mata feshi da kyau. Tsabar za ta fara fitowa cikin kwanaki 14. Lokacin da ciyawar ta kai tsawon santimita 10, sai a yi mata firi. Idan akwai wurin da shukar ba ta fito ba sai ka sake shuka wata a wurin da babu komai. Idan kana da buqatar kyakkyawar shimfixar ciyawa, sai ka yi noma sau xaya ko sau biyu a duk cikin mako biyu har zuwa Satumba.

b) Yi amfani da ciyawa mai kama da tayil a shingenka

Wannan ya fi sauri, to amma ya fi tsada. Duk da haka ta fi zama mai inganci sabo da yawancin kamfanoni masu sayar da ciyawar mai kama da tayil, suna yin ragi a farashinsu. Farashin wannan ciyawa, har kuxin aiki, yakan kama daga Yuro 5 akan murabba’in mita 2 (ya danganta da yanayinta)

2. Gyaran tsohon shinge

Ka share duk busassun ganyayyaki da matattun ciyayi duk lokacin marka (ya danganta da yanayi a Turai daga Maris zuwa Mayu). Sannan sai ka shuka tsaba idan ya zama lallai. Rava na iya sanadin cirewar wasu shuke-shuke a lokacin hunturu kuma sai ya zama ya fi dacewa ka yi aikin gyaran lokacin marka.

Gyaran shingenka ya danganta da kyan qasar wajen. Sabo da haka, za ka iya samar da abin aiki na kanka. Ka xauki falankin katako mai tsawon santimita 2–3, ka kafa qusoshi masu tsawon santimita 10 ta yadda kaifinsu zai fita ta cikin katakon. Ka lura tazarar ko wace qusa ya zama santimita 2–3. Ka saka mariqin katako ga shukar (ya kasance tsawonta ya kai kamar naka ta yadda za ka iya sarrafa ta).

To yanzu ka vauki falankin ka saka shi a shingen (bayan nomewa) ka tsaya sosai akan falankin. Yanzu sai ka ciro shi sannan ka maimaita haka har ka gama duk shingen. Za ka iya amfani da manjagara. Idan kana so ka jiqa shingenka, kana iya yin haka bayan gyaran. Ruwa zai kai ga jijiyoyi cikin sauqi.

Printed from neznama adresa