Qwara mai jure rava Rhapidophyllum hystrix (Qwara Mai Allura)

picture

Rhapidophyllum hystrix

Rhapidophyllum hystrix xaya ce daga ire-iren qwara mai jure rava. Akwai nau’i qwaya xaya na wannan shuka Rhapidophyllum. Wurin da wannan shuka tafi fitowa shine Kudu maso Gabacin Amurka. To amma, godiya ga juriyarta wadda ya kai qasa da 20 °C shuka ce sananniya a duniya, musamman a Turai.

picture

tsabar kwakwa mai allura (Rhapidophyllum hystrix)

Irin qwara ne kawai yake fitowa da tsawon mita 1–3 kuma ke da kyan jiki. Shukar Rhapidophyllum Hystrix qwara ce mai yin rassa tun daga jijiyarta, wadda waxannan jijiyoyi kan zama kamar babbar rumfa mai faxi. Zuwa wani lokaci sai jijiyoyin su zama kamar wata surquqiya mai duhu. Qwara mai allura bata yin gangar jiki a maimakon haka takanyi babbar malafa wadda kan fito har zuwa tsawon mita 1,2 da kuma faxi na kimanin santimita 17,8. Jijiyoyin kan haxa da ruvavvun ganyayyaki, vawo, da guntayen qirare. Yawancinsu miqaqqu ne a cakuxe waje guda; sukan jingina da juna ko su fito a kaikaice domin qoqarin samun hasken rana da walawa. Lokacin da ko wace saiwa ke girma, sai wasu sababbin saiwoyi su fito ta tsakanin ganyayyakin. Ana shuka irin a jiqaqqiyar qasa kuma a ajiye a wuri mai ximin da ya kai kimanin 20 °C. A shekaru 3 na farko, yana da kyau a kawar da jaririyar qwarar daga rava. Qwara mai allura tana son wuri mai danshi a rana ko kuma a inuwa, to amma ta fi son rana a yayin da sanyi ke qaruwa. Ta fi kyan gani idan ya kasance rabinta na rana rabi kuma na inuwa. Idan kuwa dukkaninta tana cikin rana babbar malafar da tayi na iya motsewa a sakamakon haka ganyenta na iya canja launi. Shukar da ta yi sama da shekara 3 ana iya ajiye ta a waje cikin lambu a duk tsawon shekara idan sanyin wurin bai yi qasa da 10 °C ba. A wurare masu sanyi, kana da buqatar samar da tsaro na ximi a yanayin da ximin ya gaza 10 °C. A matsayinta na shuka mai jure rava tana buqatar qasa tatacciya kuma a dasata a vangaren kudu. Babban abokin adawar wannan shuka shi ne a lokacin hunturu ba wai rava ba ce sai dai qasa jiqaqqiya wadda ta wuce kima. Idan yanayin sanyi ya haxu tare da kuma ruwa mai yawa za su iya kashe jijiyoyin. Wannan shuka na iya jure rava har zuwa –15 zuwa –20 °C. Yanayin sanyin da wannan shuka kan jure kan kai qasa da –28 °C.

Qwara mai jure rava domin sayarwa

Printed from neznama adresa