Welwitschia mirabilis – noman matacciyar shuka mai rai

picture

Welwitschia (Welwitschia mirabilis) tsahuwar shuka ce mai fitowa a gefen kogin Atlantika a Qasar Namibiya Kudancin Angola. Welwitschia a haqiqa bashiya ce, duk da cewa a fisge ba ta kama da bishiya. Gaba xayan shukar tana da gangar jiki guda xaya wanda ganye biyu ke fita – wannan yana kama da tsakiya wadda gefunanta bai haxu ba. Welwitschia wani lokaci tana kama da tarin shara!

picture

A ko wane lokaci wannan shuka a yanayin tsirowa ta ke (ko da a lokaci marar daxi) – wanda yake da wahala ga shuke-shuke. Welwitschia ire ne mai aure sabo da haka shuka biyu ce (namiji da macen shuka) ta zama lallai wajen yin ‘ya’ya. Akwai fure a kwanson (kamar na bishiyar pine ko sikads) wanda ke gefen ganyaye.

Kwanson tamata yana fashewa bayan ya nuna sannan ya saki wata tsaba mai tashi, wadda iska ke xauka ta warwatsa shi.

Tana cikin tsofaffin shuka – Gnetophyta, wadda ta yi kama da conifers (Pinophyta). Gnetophyta nau’i 3 ce a yadda suke bayyana: Gnetum – lianas mai manya-manyan ganye, Ephedra – gajeriyar bishiya da kuma Welwitschia da kanta.

Welwitschia ta samo sunanta daga wani masanin shuke-shuke na Sloven mai suna Friedrich Welwitsch wanda ya binciko ta a shekara ta 1860. To amma Welwitschia ba’a saka ta a bajon qasar Namibiya ba.

picture

Welwitschia ta dace da jure yanayin Hamada. Bata dogara da ruwan sama ba to amma na samun ruwa ne daga tiririn da ke fitowa daga teku. Wannan bayanin ya kamata ka sani idan kana son shuka Welwitschia. Dalilin da yasa noman Welwitschia ke haxuwa da cikas shi ne idan aka bata ruwa mai yawa sai ta ruve. Sabo da haka sai dai a shuka tsabarta a rairaiyi mai haxe da qananan duwatsu (qwayar irin yana kaiwa murabba’in milimita 2–5) sabo da yawan bayar da ruwa shi ne babbar matsala. Wajen bayar da ruwa ga Welwitschia sai anyi taka-tsan-tsan – kuma yana da kyau a yayyafa. Tsaba kan fito cikin mako guda. Za’a iya shuka ta a jikin taga mai kallon kudu. Shuka Welwitschia na buqatar juriya domin wannan shuka na fitowa a hankali – gaskiyar magana bishiya ce ta da. Idan ta sami cikakken haske da kuma ruwa kaxan, shukar za ta daxe.

Printed from neznama adresa