Noman ciyawar kifi (Pleurotus ostreatus)
Ciyawar kifi (Pleurotus ostreatus) sananniya ce a ‘yan kwanakinnan fiye da ciyawa game-gari (ciyawar champignon)! Dangantaka da ciyawa game-gari, Ciyawar kifi ta na da wata rana guda xaya – ba ta rikicewa da ciyawa mai guba “hular mutuwa” (Amanita phalloides).
Cherimoya (Annona cherimola)
Abin sha’awa a halin yanzu ana shigo da kayayyakin marmari na qasashe masu zafi zuwa Turai. Na sami nasarar sayen xan itacen cherimoya kuma na xanxana shi. Ba’a samun sa a shaguna to amma godiya ga xanxanawar da nayi, nan gaba za’a sami wannan xan itace a shago!
Asabar 23.12.2023 19:30 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare
Kiwano (Cucumis metuliferus)
Kiwano xan itace mai kama da lemon zaqi na da tsawon santimita 10–15. Yana cikin dangin gurji. ‘Ya’yan itatuwan na da zankwaye a vawonsu yadda zai tunawa mutum yanayin kayan yaqi irin na mutanen da. Tsakiyar xan itacen kore ne kuma na da ‘ya’ya a cikinsa masu tsawon milimita 5–10. Lokacin da bai nuna ba xan icen kore ne.
Asabar 23.12.2023 19:20 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare
Yaya za kayi da nomammiyar ciyawa?
Idan kana buqatar kyakkyawa, ciyawar da aka aske, sai akai-akai kana nome shingenka. Saurara kaxan, ciyawar da aka nome kan bayar da ciyawa mai yawa wanda wannan matsala ne gareka. Mafi yawan manoman da na sani kan yi maganin ciyawarsu daga sharar gidansu. Sai kawai in girgiza kaina cikin mamakin yadda ake asarar taki mai sauqi!
Ta yaya za ka nome lambunka dai dai?
Ya zama wajibi ka san yadda za ka nome lambunka dai dai domin samun ciyawa mai kyau. Babu bishiya mai yanayin qwai da zata yi kyau idan lambu ba shi da kyau!
Shuke sabon shinge
A Turai lokacin da yafi dacewa da shuke sabon shinge ko kuma shuka qarin ciyawa a shingen da ake da shi ya fara daga watan Mayu zuwa Yuni. Idan aka sami qarancin ruwan sama da marka, watan Yuli na iya zama lokaci mafi dacewa.
Kwakwar tsaunin Boliviya (Parajubaea torallyi)
Parajubaea torallyi kyakkyawar kwakwa ce daga Kudancin Amurka. To amma, ba safai manoma ke noma ta a wajen wurinta na ainihi ba, Boliviya, sabo da girman tsabarta (wannan yana nufin tsadar sufuri)
‘Yar ainihin Boliviya, tana fitowa a wuri busasshe, kuma mai qura, a zazar inter-Andea a wuri mai mita 2700–3400 a sama da kogi. Sabo da haka, kwakwar ita ce irin kwakwa mai fita a wannan yanayi a duk duniya. Yanayin zafi da wahala ya kai sama da 20 °C kuma ravar dare kan zuba babu qaqqautawa. Wasu lokuta yanayin sanyin wurin kanyi qasa da –7 °C a lokacin watannin hunturu (Yuli da Agusta) kuma ruwan sama milimita 550 ne kawai.
Dangane da KPR
Yi musayar ra'ayinka dangane da noman shuke-shuke. Rubuta batu akan lambu, shuke-shuke, noman shuke-shuke da sauransu kuma ka buga shi a yarenka a mujallarmu ta Botanix! Ka tuntuvemu domin qarin bayani.
Category: Duk Bado Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya Ciyawa Dokoki akan noman shuke-shuke Kwakwa Qwari Shuke-shuken qasashen qetare Shuke-shuken ruwa