Archive of all articles
There you can find all articles which are available in this language section of Botanix.
Category: Duk Bado Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya Ciyawa Dokoki akan noman shuke-shuke Kwakwa Qwari Shuke-shuken qasashen qetare Shuke-shuken ruwa
2023
Disamba (22)Welwitschia mirabilis – noman matacciyar shuka mai rai
Welwitschia (Welwitschia mirabilis) tsahuwar shuka ce mai fitowa a gefen kogin Atlantika a Qasar Namibiya Kudancin Angola. Welwitschia a haqiqa bashiya ce, duk da cewa a fisge ba ta kama da bishiya. Gaba xayan shukar tana da gangar jiki guda xaya wanda ganye biyu ke fita – wannan yana kama da tsakiya wadda gefunanta bai haxu ba. Welwitschia wani lokaci tana kama da tarin shara!
Lahadi 24.12.2023 07:45 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare
Bishiyar Taba (Nicotiana glauca) – bishiyar kan baranda abar hange daga nesa!
Bishiyar Taba (Nicotiana glauca)
Buqatar xan adam ta sabon abu, mai ban mamaki da abin da yake ba-saban-ba taqaitacce ne. Sabo da haka, manoman lambu ke mafarkin wani abu sabo a lambunsu – wani abu wanda ba kowa ya ke da shi ba. Da wannan dalili Kasuwar shuke-shuke ke bawa manoma wani abu sabo a duk shekara – domin kwantar da qishirwar da manoma ke da ita wajen samun abu na asali. Gabatar da sababbin ire-ire zai sanya shukar bishiyar taba ta shiga duk hannun manoma ba da daxewa ba.
Lahadi 24.12.2023 07:42 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare
Qwara mai jure rava Rhapidophyllum hystrix (Qwara Mai Allura)
Rhapidophyllum hystrix
Rhapidophyllum hystrix xaya ce daga ire-iren qwara mai jure rava. Akwai nau’i qwaya xaya na wannan shuka Rhapidophyllum. Wurin da wannan shuka tafi fitowa shine Kudu maso Gabacin Amurka. To amma, godiya ga juriyarta wadda ya kai qasa da 20 °C shuka ce sananniya a duniya, musamman a Turai.
Noman Mangwaro daga tsaba
Ka shuka sabuwar tsaba domin samun kyakkyawar tsirowa. Ka jiqa tsabar a ruwa mai ximin kimanin 20–25 °C zuwa kimanin awa 2–6.
Lahadi 24.12.2023 07:34 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare, Dokoki akan noman shuke-shuke
Mangwaron Kalimantan, Kasturi (Mangifera casturi)
Mangwaron Kalimantan (Mangifera casturi) wanda a gargajiyance aka fi sani da Kasturi bishiya ce da ake samu a wurare ‘yan qalilan mai tsawon kimanin mita 10–30 mai fita a qasashe masu zafi a zagayen Banjarmasin a kudancin Borneo (Indonisiya). A halin yanzu babu bishiyar a daji sabo da haramtattun masu saran bishiya. To amma, a wasu lokutan ana noma ta a waxannan wurare sabo da ‘ya’yanta da ke da daxi.
Lahadi 24.12.2023 07:32 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare
Mangwarorin Indonisiya
Fragrant Mango (Mangifera odorata)
A tsibirin Borneo na Indonisiya akwai ire-iren Mangwaro 34 (Mangifera) wanda ya ke fitowa a tsibirin. Yawancin waxannan ire-ire na fuskantar barazanar vacewa sabo da gurgusowar hamada. Wasu daga ire-iren Mangwaron, misali Mangwaron Kalimantan (Mangifera casturi) tuni ya vace daga daji.
Lahadi 24.12.2023 07:30 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare
Lotun xin Hindiya (Nelumbo nucifera)
Fulawar Lotus xin Hindiya
Lotus xin Hindiya (Nelumbo nucifera) bishiyar ruwa ce mai kyau ganyenta kore ne wanda yakan taso akan ruwa. Fulawarta mai ruwan hoda ana samunta a jikin reshe ta xago santimita da yawa a saman ruwa.
Ana xaukar Fulawar Lotus xin Hindiya da matuqar girmamawa musamman lokacin bukunkuna ga mabiya addinin Buda. Shukar ta dace da ci a wajen xan adam; duk da cewa ana amfani da tsabar da kuma saiwarta a wajen shirya abincin gargajiya a baki xayan Gabas maso Kudancin Asiya. Ana noma Lotus xin Hindiya kamar yadda ake shuka bado. Babu wahala wajen noma wannan shuka a yanayinmu; sai dai kawai mutum ya san yaya ake yi!
Lahadi 24.12.2023 07:24 | buga | Shuke-shuken ruwa
Noman shukar clover mai ganye huxu (Marsilea quadrifolia)
Shuka Mai Ganye Huxu (Marsilea quadrifolia) shukar ruwa ce da ganyenta yayi kama da na clovers. Ko ka san sunan shukar ruwa da clover ba su da dangantaka? Savanin haka – duk sunayen na kwatanta wasu xabi’oi ne na waxannan shuke-shuken ado masu ban mamaki waxanda ba safai akan gansu a lambu ba a duniya.
Lahadi 24.12.2023 07:19 | buga | Shuke-shuken ruwa
Pongamia pinnata Bishiyar Bakin Kogi ta Hindiya
Pongamia pinnata
Bishiyar Bakin Kogi ta Hindiya Pongamia pinnata (waxansu sunayen gargajiya: Bishiyar Honge, Bishiyar Pongam, Panigrahi) bishiya ce ta surquqiyq, mai kimanin tsawon mita 15–25, abar dangantawa da dangin bishiyar Fabaceae. Samanta yana da faxi wanda ya qunshi fararen fulawowi, ruwan hoda ko ruwan goro. Asalinta daga Hindiya ne, to amma an fi nomata a Kudu maso Gabacin Asiya.
Lahadi 24.12.2023 07:14 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare
Ganyen shayin Sin – noma ganyen shayin ka!
Tsabar ganyen shayi
Kafin qarshen hunturu ya qarato, duk manomin lambu yana tunanin mai zai noma a kaka mai zuwa. Zai fi sauqi a noma tumatir, yaji, ko kuma gurji? Ko kuma kana buqatar wani abu? Wani abu daga qasashen waje? Me kake gani game da noman ganyen shayi a bana?!
Lahadi 24.12.2023 07:12 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare
Bishiyar Khasi Pine (Pinus kesiya)
Bishiyar Khasi Pine (Pinus kesiya) iri ne mai saurin fitowa daga Asiya, wadda ba’a nomata a wani wuri daban. Bishiyarta kan kai tsawon kimanin mita 30–35 da kuma kaurin gangar jiki mai murabba’in mita 1. Ko wane reshe na da vangarori uku – ko wane xaya kimanin tsawon santimita 15 zuwa 20. ‘Ya’yan itacen wannan bishiya (cones) suna kaiwa tsawon kimanin santimita 5 zuwa 9 kuma tsawon tsabar ya kai kimanin santimita 1,5 zuwa 2,5.
Asabar 23.12.2023 20:45 | buga | Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya
Shuka fulawa mai siffar qwai da yabanya
Fitar da fulawa mai siffar qwai da yabanya wadda ka karva daga cikin maqunshinta ta hanyar saqon waya, kuma ka barta a inuwa har zuwa wasu kwanaki 2–3. Ta wani vangaren kana iya shuka su nan take kuma ka ajiye su a inuwa zuwa wasu kwanaki ta yadda zafin rana ba zai tava su kai tsaye ba.
Asabar 23.12.2023 20:41 | buga | Dokoki akan noman shuke-shuke
Burodin xan itace Artocarpus odoratissimus, Marang
Genus Burodin xan itace (Artocarpus) bishiya ce da ta qunshi kimanin ire-ire 60 na bishiyoyin yanayin qasashe masu zafi dangin Moraceae (dangin bishiyar da aka fi sani da mulberry ko kuma fig). Ana samun su a Kudu maso gabas na Asiya da kuma tsibiran Tekun Pacific. Burodin xan itace na da dangantaka da Ficus (fig trees). Bishiyar Burodin xan itace da aka fi nomawa ita ce Artocarpus altilis. Yawancin sauran ire-iren kamar Artocarpus communis, Artocarpus integer (Cempedak), Artocarpus heterophyllus (Jackfruit, Nangka) kuma Artocarpus odoratissimus (Marang) su ma vangare ne na dangin Burodin xan itace.
Asabar 23.12.2023 20:29 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare
Yaya za ka yi maganin qwaron wake?
Ina zato ba sai na gabatar maka da qwaron wake ba. Wannan wani qaramin qwaro ne girmansa milimita 3–4, da ake samu a tsaba a cikin xakin girki ga misali.
Wannan maxarnacin qwaro yana haifuwa a duk tsaba mai kwanso. A gaskiyance, duk wata tsaba mai kwanso na da wasu daga cikin wannan halitta – gujiya – qwaron gujiya (qwaro), jinvirin wake – qwaron jinvirin wake, lentils – qwaron lentils, waken lambu – kwaron waken lambu da sauransu.
NOVODOR FC domin yaqi da qwarin dankalin Kwalarado
Ba na zato sai na gabatar da qwaron dankalin Kwalarado (Leptinotarsa decemlineata) domin kowa ya san wannan babban qwaro mai lalata dankali kuma wanda yake da wahalar kashewa ba tare da sinadarai ba. A wani lokaci, babu wanda ya san yadda za’a yi maganin wannan qwaro na dankalin Kwalarado.
Noman ciyawar kifi (Pleurotus ostreatus)
Ciyawar kifi (Pleurotus ostreatus) sananniya ce a ‘yan kwanakinnan fiye da ciyawa game-gari (ciyawar champignon)! Dangantaka da ciyawa game-gari, Ciyawar kifi ta na da wata rana guda xaya – ba ta rikicewa da ciyawa mai guba “hular mutuwa” (Amanita phalloides).
Cherimoya (Annona cherimola)
Abin sha’awa a halin yanzu ana shigo da kayayyakin marmari na qasashe masu zafi zuwa Turai. Na sami nasarar sayen xan itacen cherimoya kuma na xanxana shi. Ba’a samun sa a shaguna to amma godiya ga xanxanawar da nayi, nan gaba za’a sami wannan xan itace a shago!
Asabar 23.12.2023 19:30 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare
Kiwano (Cucumis metuliferus)
Kiwano xan itace mai kama da lemon zaqi na da tsawon santimita 10–15. Yana cikin dangin gurji. ‘Ya’yan itatuwan na da zankwaye a vawonsu yadda zai tunawa mutum yanayin kayan yaqi irin na mutanen da. Tsakiyar xan itacen kore ne kuma na da ‘ya’ya a cikinsa masu tsawon milimita 5–10. Lokacin da bai nuna ba xan icen kore ne.
Asabar 23.12.2023 19:20 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare
Yaya za kayi da nomammiyar ciyawa?
Idan kana buqatar kyakkyawa, ciyawar da aka aske, sai akai-akai kana nome shingenka. Saurara kaxan, ciyawar da aka nome kan bayar da ciyawa mai yawa wanda wannan matsala ne gareka. Mafi yawan manoman da na sani kan yi maganin ciyawarsu daga sharar gidansu. Sai kawai in girgiza kaina cikin mamakin yadda ake asarar taki mai sauqi!
Ta yaya za ka nome lambunka dai dai?
Ya zama wajibi ka san yadda za ka nome lambunka dai dai domin samun ciyawa mai kyau. Babu bishiya mai yanayin qwai da zata yi kyau idan lambu ba shi da kyau!
Shuke sabon shinge
A Turai lokacin da yafi dacewa da shuke sabon shinge ko kuma shuka qarin ciyawa a shingen da ake da shi ya fara daga watan Mayu zuwa Yuni. Idan aka sami qarancin ruwan sama da marka, watan Yuli na iya zama lokaci mafi dacewa.
Kwakwar tsaunin Boliviya (Parajubaea torallyi)
Parajubaea torallyi kyakkyawar kwakwa ce daga Kudancin Amurka. To amma, ba safai manoma ke noma ta a wajen wurinta na ainihi ba, Boliviya, sabo da girman tsabarta (wannan yana nufin tsadar sufuri)
‘Yar ainihin Boliviya, tana fitowa a wuri busasshe, kuma mai qura, a zazar inter-Andea a wuri mai mita 2700–3400 a sama da kogi. Sabo da haka, kwakwar ita ce irin kwakwa mai fita a wannan yanayi a duk duniya. Yanayin zafi da wahala ya kai sama da 20 °C kuma ravar dare kan zuba babu qaqqautawa. Wasu lokuta yanayin sanyin wurin kanyi qasa da –7 °C a lokacin watannin hunturu (Yuli da Agusta) kuma ruwan sama milimita 550 ne kawai.
Dangane da KPR
Yi musayar ra'ayinka dangane da noman shuke-shuke. Rubuta batu akan lambu, shuke-shuke, noman shuke-shuke da sauransu kuma ka buga shi a yarenka a mujallarmu ta Botanix! Ka tuntuvemu domin qarin bayani.
Category: Duk Bado Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya Ciyawa Dokoki akan noman shuke-shuke Kwakwa Qwari Shuke-shuken qasashen qetare Shuke-shuken ruwa