Archive of all articles
There you can find all articles which are available in this language section of Botanix.
Category: Duk Bado Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya Ciyawa Dokoki akan noman shuke-shuke Kwakwa Qwari Shuke-shuken qasashen qetare Shuke-shuken ruwa
2023
Disamba (22)Vangare: Shuke-shuken qasashen qetare
Shuke-shuken qasashen qetare
Welwitschia mirabilis – noman matacciyar shuka mai rai
Welwitschia (Welwitschia mirabilis) tsahuwar shuka ce mai fitowa a gefen kogin Atlantika a Qasar Namibiya Kudancin Angola. Welwitschia a haqiqa bashiya ce, duk da cewa a fisge ba ta kama da bishiya. Gaba xayan shukar tana da gangar jiki guda xaya wanda ganye biyu ke fita – wannan yana kama da tsakiya wadda gefunanta bai haxu ba. Welwitschia wani lokaci tana kama da tarin shara!
Lahadi 24.12.2023 07:45 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare
Bishiyar Taba (Nicotiana glauca) – bishiyar kan baranda abar hange daga nesa!
Bishiyar Taba (Nicotiana glauca)
Buqatar xan adam ta sabon abu, mai ban mamaki da abin da yake ba-saban-ba taqaitacce ne. Sabo da haka, manoman lambu ke mafarkin wani abu sabo a lambunsu – wani abu wanda ba kowa ya ke da shi ba. Da wannan dalili Kasuwar shuke-shuke ke bawa manoma wani abu sabo a duk shekara – domin kwantar da qishirwar da manoma ke da ita wajen samun abu na asali. Gabatar da sababbin ire-ire zai sanya shukar bishiyar taba ta shiga duk hannun manoma ba da daxewa ba.
Lahadi 24.12.2023 07:42 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare
Noman Mangwaro daga tsaba
Ka shuka sabuwar tsaba domin samun kyakkyawar tsirowa. Ka jiqa tsabar a ruwa mai ximin kimanin 20–25 °C zuwa kimanin awa 2–6.
Lahadi 24.12.2023 07:34 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare, Dokoki akan noman shuke-shuke
Mangwaron Kalimantan, Kasturi (Mangifera casturi)
Mangwaron Kalimantan (Mangifera casturi) wanda a gargajiyance aka fi sani da Kasturi bishiya ce da ake samu a wurare ‘yan qalilan mai tsawon kimanin mita 10–30 mai fita a qasashe masu zafi a zagayen Banjarmasin a kudancin Borneo (Indonisiya). A halin yanzu babu bishiyar a daji sabo da haramtattun masu saran bishiya. To amma, a wasu lokutan ana noma ta a waxannan wurare sabo da ‘ya’yanta da ke da daxi.
Lahadi 24.12.2023 07:32 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare
Mangwarorin Indonisiya
Fragrant Mango (Mangifera odorata)
A tsibirin Borneo na Indonisiya akwai ire-iren Mangwaro 34 (Mangifera) wanda ya ke fitowa a tsibirin. Yawancin waxannan ire-ire na fuskantar barazanar vacewa sabo da gurgusowar hamada. Wasu daga ire-iren Mangwaron, misali Mangwaron Kalimantan (Mangifera casturi) tuni ya vace daga daji.
Lahadi 24.12.2023 07:30 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare
Pongamia pinnata Bishiyar Bakin Kogi ta Hindiya
Pongamia pinnata
Bishiyar Bakin Kogi ta Hindiya Pongamia pinnata (waxansu sunayen gargajiya: Bishiyar Honge, Bishiyar Pongam, Panigrahi) bishiya ce ta surquqiyq, mai kimanin tsawon mita 15–25, abar dangantawa da dangin bishiyar Fabaceae. Samanta yana da faxi wanda ya qunshi fararen fulawowi, ruwan hoda ko ruwan goro. Asalinta daga Hindiya ne, to amma an fi nomata a Kudu maso Gabacin Asiya.
Lahadi 24.12.2023 07:14 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare
Ganyen shayin Sin – noma ganyen shayin ka!
Tsabar ganyen shayi
Kafin qarshen hunturu ya qarato, duk manomin lambu yana tunanin mai zai noma a kaka mai zuwa. Zai fi sauqi a noma tumatir, yaji, ko kuma gurji? Ko kuma kana buqatar wani abu? Wani abu daga qasashen waje? Me kake gani game da noman ganyen shayi a bana?!
Lahadi 24.12.2023 07:12 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare
Burodin xan itace Artocarpus odoratissimus, Marang
Genus Burodin xan itace (Artocarpus) bishiya ce da ta qunshi kimanin ire-ire 60 na bishiyoyin yanayin qasashe masu zafi dangin Moraceae (dangin bishiyar da aka fi sani da mulberry ko kuma fig). Ana samun su a Kudu maso gabas na Asiya da kuma tsibiran Tekun Pacific. Burodin xan itace na da dangantaka da Ficus (fig trees). Bishiyar Burodin xan itace da aka fi nomawa ita ce Artocarpus altilis. Yawancin sauran ire-iren kamar Artocarpus communis, Artocarpus integer (Cempedak), Artocarpus heterophyllus (Jackfruit, Nangka) kuma Artocarpus odoratissimus (Marang) su ma vangare ne na dangin Burodin xan itace.
Asabar 23.12.2023 20:29 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare
Cherimoya (Annona cherimola)
Abin sha’awa a halin yanzu ana shigo da kayayyakin marmari na qasashe masu zafi zuwa Turai. Na sami nasarar sayen xan itacen cherimoya kuma na xanxana shi. Ba’a samun sa a shaguna to amma godiya ga xanxanawar da nayi, nan gaba za’a sami wannan xan itace a shago!
Asabar 23.12.2023 19:30 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare
Kiwano (Cucumis metuliferus)
Kiwano xan itace mai kama da lemon zaqi na da tsawon santimita 10–15. Yana cikin dangin gurji. ‘Ya’yan itatuwan na da zankwaye a vawonsu yadda zai tunawa mutum yanayin kayan yaqi irin na mutanen da. Tsakiyar xan itacen kore ne kuma na da ‘ya’ya a cikinsa masu tsawon milimita 5–10. Lokacin da bai nuna ba xan icen kore ne.
Asabar 23.12.2023 19:20 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare
Dangane da KPR
Yi musayar ra'ayinka dangane da noman shuke-shuke. Rubuta batu akan lambu, shuke-shuke, noman shuke-shuke da sauransu kuma ka buga shi a yarenka a mujallarmu ta Botanix! Ka tuntuvemu domin qarin bayani.
Category: Duk Bado Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya Ciyawa Dokoki akan noman shuke-shuke Kwakwa Qwari Shuke-shuken qasashen qetare Shuke-shuken ruwa