Botanix – Mujalla akan shuke-shuke

Botanix Hausa

Burodin xan itace Artocarpus odoratissimus, Marang

Genus Burodin xan itace (Artocarpus) bishiya ce da ta qunshi kimanin ire-ire 60 na bishiyoyin yanayin qasashe masu zafi dangin Moraceae (dangin bishiyar da aka fi sani da mulberry ko kuma fig). Ana samun su a Kudu maso gabas na Asiya da kuma tsibiran Tekun Pacific. Burodin xan itace na da dangantaka da Ficus (fig trees). Bishiyar Burodin xan itace da aka fi nomawa ita ce Artocarpus altilis. Yawancin sauran ire-iren kamar Artocarpus communis, Artocarpus integer (Cempedak), Artocarpus heterophyllus (Jackfruit, Nangka) kuma Artocarpus odoratissimus (Marang) su ma vangare ne na dangin Burodin xan itace.

A wannan batu za mu gabatar muku da Marang (Artocarpus odoratissimus). Bishiya ce mai ni’ima daga Tsibiran Borneo na Qasar Indonisiya. To amma, ana noma ta domin siyarwa a qanan kasuwanni a maqotan qasashe kamar Malesiya, Tailan, da kuma Phillipines. A yaren waxannan qasashe ana kiranta Atau, Keiran, Loloi, Madang, Marang, Pi-ien, Pingan, Tarap, Terap, and Khanun Sampalor. Wannan iri ba’a sanshi a wajen waxannan qasashe ba. A daji, tana fitowa a rairayi a dazuka murabba’in mita 1000 sama da matakin kogi.

Bishiyar Artocarpus odoratissimus na kaiwa tsawon mita 25; kuma ganyenta yana kaiwa daga tsawon santimita 16 zuwa 50 da kuma faxin santimita 11 zuwa 28.

Wannan bishiya xaya-ce-tamkar-dubu, qwaya xaya na iya samar da ‘ya’ya. ‘Ya’yan wannan bishiya tsanwa ne, masu yanayin qwai.

Bishiyar Burodin xan itace na da mahimmanci ga mutanen Kudu maso Gabacin Asiya wajen samr da abinci. Cikin ‘ya’yan wannan bishiya fari ne fes, kuma suna da zaqi, daxi, qanshi kamar na Gawasa (Durio, xan itace mafi qanshi a duniya).

Hanya mafi kyau ta yaxa Marang Artocarpus odoratissimus ita ce ta hanyar tsaba. Sabuwar tsaba na fitowa da kyau kuma yabanya ta fita cikin sati xaya. To amma, ingancin irin na iya raguwa idan aka ajite shi har kimanin mako uku. Sabo da haka, a shuka iri a rairayi, tatacce da zaran an girbe shi. Yana da wahala a yaxa shi ta hanyar shuka kuma kwari da cutuka kan yi illa da waxannan bishiyoyi.

Burodin xan itace ba ta jurewa rava. Sabo da shuka ce da ta samo asali daga qasashe masu zafi kada yanayin da za’a ajiye ta ya zama mai sanyi sosai qasa da 7 °C. A wurare masu zafi ko masu zafi kaxan ana iya noma Burodin xan itace a lambu, to amma sai dai a cikin wuri ko kuma xaki na musamman domin gudun rava. 

picture

Xan itacen Marang Artocarpus odoratissimus, Borneo, Indonesia

picture

Xan itacen Marang Artocarpus odoratissimus, Borneo, Indonesia

picture

Xan itacen Marang Artocarpus odoratissimus, Borneo, Indonesia

picture

Cikakken bayanin xan itacen Marang Artocarpus odoratissimus, Borneo, Indonesia

picture

Cikakken bayanin xan itacen Marang Artocarpus odoratissimus, Borneo, Indonesia

picture

Cikakken bayanin xan itacen Marang Artocarpus odoratissimus, Borneo, Indonesia

««« Batun baya: Yaya za ka yi maganin qwaron wake? Batun gaba: Shuka fulawa mai siffar qwai da yabanya »»»

Asabar 23.12.2023 20:29 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare

Dangane da KPR

Logo of KPR - Qungiyar Manoman Lambu ta Slovakiya
KPR - Qungiyar manoman lambu qungiya ce ta qasa-da-qasa. Qara karatu...
Yi musayar ra'ayinka dangane da noman shuke-shuke. Rubuta batu akan lambu, shuke-shuke, noman shuke-shuke da sauransu kuma ka buga shi a yarenka a mujallarmu ta Botanix! Ka tuntuvemu domin qarin bayani.

Category: Duk Bado Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya Ciyawa Dokoki akan noman shuke-shuke Kwakwa Qwari Shuke-shuken qasashen qetare Shuke-shuken ruwa