Shuka fulawa mai siffar qwai da yabanya
Fitar da fulawa mai siffar qwai da yabanya wadda ka karva daga cikin maqunshinta ta hanyar saqon waya, kuma ka barta a inuwa har zuwa wasu kwanaki 2–3. Ta wani vangaren kana iya shuka su nan take kuma ka ajiye su a inuwa zuwa wasu kwanaki ta yadda zafin rana ba zai tava su kai tsaye ba.
Shukar yabanya
Yi xan qaramin rami wanda za ka shuka yabanya a ciki. Fitar da yabanyar daga cikin tukunya (ko kuma daga jakar leda idan an aiko su ne a rarrabe), juya saiwoyin qasa sannan ka rarraba su kafin ka saka shukar a rami.
Zuba ruwa acikin ramin, sannan bayan qasa ta shanye duk ruwan, ka sake zuba wani ruwan. Ka yiwa sauran shuke-shuken haka. Bayan ka gama da dukkaninsu sai ka sake zubawa.
A ‘yan kwanaki masu zuwa bayan dashen, za ka dinga basu ruwa gwargwadon buqatarsu kuma ka lura karka ajiye su a cikin rana mai qarfi. Shuke-shuken za su yi saiwa cikin makwanni 1–3 bayan nan sai ka dinga kula da su kamar dai yadda ka ke kula da sauran shuke-shuke na lambunka.
Shuka fulawa mai siffar qwai da yabanya
Da farko ka fara karce qasar wajen da ka ke so ka shuka bishiya mai yanayin qwai da kuma doya (za muyi amfani da kalmar shuka mai yanayin qwai) a gaba xayan batun).Fito da shukar mai yanayin qwai daga jakankunan takarda kafin ka shuka su. Ka gina isasshen rami ma zurfi (duga jadawali) sannan ka saka shukar mai yanayin qwai a ramin sama ya kalli sama. Wasu shuke-shuken masu yanayin qwai ba za su rayu ba idan samansu yana kallon qasa – ku lura sosai wajen shuka su dai dai!
Idan ka shuka tulip a tsakiyar bazara (wata qila ba zaka ajiye su a wani wuri ba lokacin hutu) ba sai ka basu ruwa ba. Shukar za ta huta ba zata fito ba har sai damina ta sauka. Qananan shuka mai yanayin qwai na da wahalar raino, sai a shuka ta a rami marar zurfi. Domin sanin zurfin da ya kamata ka haqa, ya zama lallai ka san tazara tsakanin saman shukar da kuma saman qasa!
Za mu ciro shukar daga cikin qasa yayin da saman (sama da rami) ya yanqwane (wannan qa’ida ce ta duk shuka mai yanayin qwai sai dai Gladiolus) – wannan zai fi dacewa a cikin watan Mayu a Turai (lokacin zafi ko bazara). Sauran ma na iyawa, bayan an ciro su daga qasa, an adanasu (idan har suna bushe) har zuwa kaka (musamman albasa, tafarnuwa, citta da tulip).
Sauran nau’oin kamar lily, inibi hyacinth (Muscari), Ornithogalum, da solomon's seal (Polygonatum) ba za’a iya ajiyarsu ta haka ba, domin ba za su rayu ba. Waxanda ba za’a iya ajiye su ba (a wuri basasshe) ana iya shuka su daga wannan wuri zuwa wancan a lambunka (za su iya rayuwa har zuwa kimanin mako guda, to amma a guji ajiye su a waje su wuce wannan lokaci).
Ire-ire | lokacin shuka lokaci | shuka zurfi a santimita |
Qanana masu ma’aunin shuka mai yanayin qwai tsawon santimita 2 kamar Allium carinatum, flavum, molly, oleraceum, scorodoprasum | 7.-10. | 5–8 |
Manya masu ma’aunin shuka mai yanayin qwai tsawon santimita 10 kamar Allium giganteum, karataviense, nigrum | 7.-10. | 10–15 |
Colchicum ire-ire masu girma da kaka | 8. | 15 |
Crocus – ire-ire masu girma da marka (Crocus chrysanthus, Crocus vernus) | 10. | 9 |
Crocus – ire-ire masu girma da kaka (Crocus sativius) | (7.-)8. | 9 |
Gladiolus (haxe-haxen lambu) | 4.-5. | 10 (qasa da 5) |
Gladiolus (ire-iren daji ‘yan asalin Afirka ta Kudu) | 9. | 5–8 |
Lilium candidum – farar lily ko Madonna lily | 8. | 3 |
Lilium – haxe-haxen lambu | 9.(-10.) | 5–15 ya danganta da yanayi |
Muscari – inibi hyacinth | 7.-10. | 8–10 |
Narcissus – narcis | 8. | 10 |
Ornithogalum umbellatum – Tauraruwar-Bethlehem, Ciyawar Lily | 7.-10. | 10 |
Polygonatum – salomons seal | 8.10., 2.-3. | 10 |
Tulips masu qananan shuka mai yanayin qwai kamar Tulipa chrysantha, harda, saxatillis, turkestanica, urumiensis | 10. | 10 |
Tulip mai manyan shuka mai yanayin qwai – Tulipa greigii, Tulipa fosteriana, Tulipa kaufmanniana da haxe-haxen lambu | 10. | 12–14 |
Yaxa shukar Lily ta hanyar ma’auni
Yaxa shukar Lily ta hanyar ma’auni
Hanya mafi sauqi ta yaxa lily ta yaxu ta hanyar ma’auni (jerin fatar shuka mai yanayin qwai)
Ka tsara ma’aunin a kunya-kunya mai zufrin santimita 1–2 (=zurfin qasar da ya haxa ma’aunin) kuma ka ajiye su a zafin a qalla 25–30 ºC idan da rana ne kuma a kimanin 22 ºC da daddare (yanayin zafi da daddare ba shi da yawa, mafi amfanin yanayin zafi shi ne na rana) a cikin misalin kwaba, gidan shuke-shuke ko jikin tagar cikin gidanka. Ka tabbata qasar busasshiya ce. Ta wannan hanya shuka mai yanayin qwai za ta girma da wuri a saman ma’aunin. A cikin wata 1–3, shuka mai yanayin qwai guda 2–3 za ta fito a ma’aunin da zai kai santimita 1! Idan ka cire ma’aunin ka shuka su a qarshen Yuli, za ka xauki waxannan sababbin shuka mai yanayin qwai daga cikin qasa a watan Satumba kuma ka shuka su a rami mai zurfin santimita 2 a cikin lambu. Ko ka wace shuka daban, kuma ka bar tazarar a qalla santimita 4 tsakaninsu – bayan shekara 4–6 za ka sami kyakkyawan tsari na fitowar shukarka!
Shuka tsabar fulawa mai yanayin qwai
Wasu daga fulawar shuka mai yanayin qwai na iya yaxuwa da gaggawa kuma musamman idan aka shuka tsabarta. A Turai lokacin da yafi dacewa na shuka tsaba mai zurfin santimita 0,5–1 a watan Maris zuwa Aprilu.
Kada ka shuka su a farkon shekara, amma ka barsu a wurin da suke. Wasu ire-iren na iya fita a kaka mai zuwa. Wasu saura kuma na iya girma shekaru 2–5 bayan shuka. Qananan shukar kuwa kan girma fiye da manya.
««« Batun baya: Burodin xan itace Artocarpus odoratissimus, Marang Batun gaba: Bishiyar Khasi Pine (Pinus kesiya) »»»
Asabar 23.12.2023 20:41 | buga | Dokoki akan noman shuke-shuke
Dangane da KPR
Yi musayar ra'ayinka dangane da noman shuke-shuke. Rubuta batu akan lambu, shuke-shuke, noman shuke-shuke da sauransu kuma ka buga shi a yarenka a mujallarmu ta Botanix! Ka tuntuvemu domin qarin bayani.
Category: Duk Bado Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya Ciyawa Dokoki akan noman shuke-shuke Kwakwa Qwari Shuke-shuken qasashen qetare Shuke-shuken ruwa