Bishiyar Khasi Pine (Pinus kesiya)
Bishiyar Khasi Pine (Pinus kesiya) iri ne mai saurin fitowa daga Asiya, wadda ba’a nomata a wani wuri daban. Bishiyarta kan kai tsawon kimanin mita 30–35 da kuma kaurin gangar jiki mai murabba’in mita 1. Ko wane reshe na da vangarori uku – ko wane xaya kimanin tsawon santimita 15 zuwa 20. ‘Ya’yan itacen wannan bishiya (cones) suna kaiwa tsawon kimanin santimita 5 zuwa 9 kuma tsawon tsabar ya kai kimanin santimita 1,5 zuwa 2,5.
Asalin bishiyar Khasi Pine (Pinus kesiya) daga shiyyar Himalaya ne: daga Arewa-maso-Gabacin Hindiya (a halin yanzu sabo da saran katako sai a Khasi Mt. da Naga Mt. a jihar Meghalay da Manipur), Sin (shiyyar Yunnan), Bama (Myanmar), Arewacin Tailan, Laos, Vietnam (Lai Chau, Lang Son, Cao Bang, Quang Ninh) da Philippines (Luzon). Wani lokaci akan xauki bishiyar Pine daga Philippines a matsayin iri daban mai suna Pinus insularis. A qasar Sin mutun na iya samun iri mai kama da wannan wanda ake kira Pine xin Yunnan (Pinus yunnanensis)
Ana samun wannan iri a magangara mai mabanbantan bishiyoyi a qasa marar inganci (mai pH na 4,5) da kuma tsawon sama da kogi na mita 800–2000 to amma yawanci yana kaiwa mita 1200–1400. Wurin yana da matsakaicin sanyi da sauye-sauyen yanayi na damina da bazara a cikin shekara. Akan sami ruwan sama mai yawa da shuke-shuke masu yawa da kuma yanayin damina da bazara a cikin shekara tare ruwan sama mai yawa da kuma gumi mai yawan 70%.
Wannan shuka na da sauqin jure rava, to amma ba ta jure rava mai yawa lokacin kaka. A lokacin girbi, tana buqatar wurin da babu rava.
Wasu sunayen wannan shuka su ne: Pinus khasya, Pinus khasyanus
««« Batun baya: Shuka fulawa mai siffar qwai da yabanya Batun gaba: Ganyen shayin Sin – noma ganyen shayin ka! »»»
Asabar 23.12.2023 20:45 | buga | Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya
Dangane da KPR
Yi musayar ra'ayinka dangane da noman shuke-shuke. Rubuta batu akan lambu, shuke-shuke, noman shuke-shuke da sauransu kuma ka buga shi a yarenka a mujallarmu ta Botanix! Ka tuntuvemu domin qarin bayani.
Category: Duk Bado Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya Ciyawa Dokoki akan noman shuke-shuke Kwakwa Qwari Shuke-shuken qasashen qetare Shuke-shuken ruwa