Botanix – Mujalla akan shuke-shuke

Botanix Hausa

Pongamia pinnata Bishiyar Bakin Kogi ta Hindiya

picture

Pongamia pinnata

Bishiyar Bakin Kogi ta Hindiya Pongamia pinnata (waxansu sunayen gargajiya: Bishiyar Honge, Bishiyar Pongam, Panigrahi) bishiya ce ta surquqiyq, mai kimanin tsawon mita 15–25, abar dangantawa da dangin bishiyar Fabaceae. Samanta yana da faxi wanda ya qunshi fararen fulawowi, ruwan hoda ko ruwan goro. Asalinta daga Hindiya ne, to amma an fi nomata a Kudu maso Gabacin Asiya.

Pongamia pinnata ba bishiyar qasashe masu zafi ba ce ko jure zafi da hasken rana. Madalla da manya-manyan jijiyoyinta, kuma ta na jure fari. Ta na fita a rairayi da kuma qasa mai tsakuyoyi, ya haxa da duwatsu, to amma wajen noma, akan iya shuka ta a kusan duk ko wace irin qasa har ma da mai gishiri-gishiri.

Wasu lokuta akan shuka ta a busassun wurare kuma akan yi amfani da ita wajen tsara qasa a matsayin mai rage qarfin iska ko kuma wajen bada inuwa. Ana amfani da rassanta wajen saqa igiya, kuma ruwan jikinta akan yi amfani da shi a zamanin da wajen magani a raunuka waxanda kifi mai guba ke haddasawa.

Jijiyoyinta kan taimaka wajen daidaita iskar nitrogen, wani mataki wanda iskar nitrogen (N2) ke canjawa zuwa NH4+ (wani yanayi na iskar nitrogen da shuka ke amafani da shi). Sabo da haka, akan yi amfani da ita wajen bunqasa gona wadda ba ta bayarda amfani mai yawa. Duk da cewa shukar na da guba, ruwan shukar, harma da mai, maganin guba ne. Man tsabar ana yin amfani da shi a matsayin man fitila, mahaxin sabulu, man inji, da man shuke-shuke.

««« Batun baya: Ganyen shayin Sin – noma ganyen shayin ka! Batun gaba: Noman shukar clover mai ganye huxu (Marsilea quadrifolia) »»»

Lahadi 24.12.2023 07:14 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare

Dangane da KPR

Logo of KPR - Qungiyar Manoman Lambu ta Slovakiya
KPR - Qungiyar manoman lambu qungiya ce ta qasa-da-qasa. Qara karatu...
Yi musayar ra'ayinka dangane da noman shuke-shuke. Rubuta batu akan lambu, shuke-shuke, noman shuke-shuke da sauransu kuma ka buga shi a yarenka a mujallarmu ta Botanix! Ka tuntuvemu domin qarin bayani.

Category: Duk Bado Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya Ciyawa Dokoki akan noman shuke-shuke Kwakwa Qwari Shuke-shuken qasashen qetare Shuke-shuken ruwa