Noman shukar clover mai ganye huxu (Marsilea quadrifolia)
Shuka Mai Ganye Huxu (Marsilea quadrifolia) shukar ruwa ce da ganyenta yayi kama da na clovers. Ko ka san sunan shukar ruwa da clover ba su da dangantaka? Savanin haka – duk sunayen na kwatanta wasu xabi’oi ne na waxannan shuke-shuken ado masu ban mamaki waxanda ba safai akan gansu a lambu ba a duniya.
Clover mai Ganye Huxu na da dogwayen reshe, wanda kan tunawa mutum da maxaurin takalma. Ganye mai tasowa akan ruwa, yana tsirowa ne daga waxannan resuna. Waxannan ganyayyaki sun kasu kaso huxu, da suka yi kama da clover mai ganye huxu. Idan ka fito da reshen daga ruwa a lokacin bazara, sai kaga wasu qananan abubuwa (suna kama da qananan wake). Daga jikin wannan shuka wasu shuke-shuken kan iya fita – wannan na nuna cewa wannan shuka na iya haifar da wasu daga jikinta. Clover Mai Ganye Huxu kan tsiro a ruwan da baya tafiya, tana da abubuwa masu gina jiki, a duk shiyyoyin duniya, amma banda Kudancin Amurka.
A Amurka, ana kallon wannan shuka a matsayin baquwa. A Slovakiya, wannan shuka na fitowa a wurare 7 a gefen tekun Latorika. A kwanakin baya, tana fitowa a Kogin Bodrog, Laborek da Uh.
A wurare masu zafi akwai ire-iren wannan shuka, akan shuka waxannan a mazubin ruwa.
Clover Mai Ganye Huxu (Marsilea quadrifolia), kafin ayi girbi, bata buqatar wani mahimmin aiki kuma za ta iya rayuwa a ko wace irin tukunya idan har an cika ta da ruwa da kuma qasa kaxan. Za ka iya shuka ta ba tare da wata matsala ba a tukunya mai santimita 20×20×20, to amma girman da aka fi so shi ne lita 60–80 ko sama da haka. Za ka iya ajiye wannan shuka a waje a duk cikin shekara (sabo da tana jure rava). Tunda ba ta buqatar abubuwa da yawa, kuma tana da saurin girma, kowa zai iya shuka ta.
Clover Mai Ganye Huxu ta fi sauqin nomawa a kududdufin da ke lambu. Kawai zuba qasa a lambunka a qasan kududdufin – sannan ka zuba resunan a cikin qasa. Bayan haka, tana buqatar kulawa kaxan, sabo da shukar Clover Mai Ganye Huxu za ta iya kula da kanta. Clover Mai Ganye Huxu na iya sabo da yawan ruwan da ta sami kanta a ciki. Za ka iya saka ta a ramuka masu mabanbantan zurfi (santimita 5–100) – gangar jikin shukar na iya sabawa da zurfin har lokacin da ganyenta zai fita saman ruwa. Zaka iya taimaka mata wajen girma ta hanyar rarraba mata rassanta. Qaramin reshe (misalin santimita 10) ya isa ya bayarda tarin Clover Mai Ganye Huxu akan ruwa.
««« Batun baya: Pongamia pinnata Bishiyar Bakin Kogi ta Hindiya Batun gaba: Lotun xin Hindiya (Nelumbo nucifera) »»»
Lahadi 24.12.2023 07:19 | buga | Shuke-shuken ruwa
Dangane da KPR
Yi musayar ra'ayinka dangane da noman shuke-shuke. Rubuta batu akan lambu, shuke-shuke, noman shuke-shuke da sauransu kuma ka buga shi a yarenka a mujallarmu ta Botanix! Ka tuntuvemu domin qarin bayani.
Category: Duk Bado Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya Ciyawa Dokoki akan noman shuke-shuke Kwakwa Qwari Shuke-shuken qasashen qetare Shuke-shuken ruwa