Botanix – Mujalla akan shuke-shuke

Botanix Hausa

Mangwarorin Indonisiya

picture

Fragrant Mango (Mangifera odorata)

A tsibirin Borneo na Indonisiya akwai ire-iren Mangwaro 34 (Mangifera) wanda ya ke fitowa a tsibirin. Yawancin waxannan ire-ire na fuskantar barazanar vacewa sabo da gurgusowar hamada. Wasu daga ire-iren Mangwaron, misali Mangwaron Kalimantan (Mangifera casturi) tuni ya vace daga daji.

Sauran ire-iren bishiyoyin Mangwro daga Borneo misalin Mangifera griffithi (wanda aka fi sani da waxannan sunaye na gargajiya: asem raba, da romian), Mangifera pajang (asem payang), Mangifera quadrifida (asem kipang) da Mangifera torquenda (asem putaran).

Fragrant Mango (Mangifera odorata) sanannen irin Mangwaro ne da ake nomawa a Kudu-maso-Gabacin Asiya. Gamin gambiza ne tsakaninsa da sauran Mangwarori (Mangifera indica) da Horse Mango (Mangifera foetida). An fi saninsa a gargajiyance da: : kuweni, kuwini (a yaren mutanen Indonisiya); kweni, asam membacang, macang, lekup (a yaren mutanen Malay); kuwini, ambacang, embacang, lakuik (a yaren mutanen Minangkabau); kuweni, kebembem (a yaren mutanen Betawi); kaweni, kawini, bembem (a yaren mutanen Sundan); kaweni, kuweni, kweni (a yaren mutanen Java); kabeni, beni, bine, pao kabine (a yaren mutanen Madurese), kweni, weni (a yaren mutanen Balinese); mangga kuini (a Arewacin Sulawesi); da kuini, guin, koini, kowini, koine, guawe stinki, sitingki, hitingki (a tsibiran Maluku).

««« Batun baya: Lotun xin Hindiya (Nelumbo nucifera) Batun gaba: Mangwaron Kalimantan, Kasturi (Mangifera casturi) »»»

Lahadi 24.12.2023 07:30 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare

Dangane da KPR

Logo of KPR - Qungiyar Manoman Lambu ta Slovakiya
KPR - Qungiyar manoman lambu qungiya ce ta qasa-da-qasa. Qara karatu...
Yi musayar ra'ayinka dangane da noman shuke-shuke. Rubuta batu akan lambu, shuke-shuke, noman shuke-shuke da sauransu kuma ka buga shi a yarenka a mujallarmu ta Botanix! Ka tuntuvemu domin qarin bayani.

Category: Duk Bado Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya Ciyawa Dokoki akan noman shuke-shuke Kwakwa Qwari Shuke-shuken qasashen qetare Shuke-shuken ruwa