Botanix – Mujalla akan shuke-shuke

Botanix Hausa

Mangwaron Kalimantan, Kasturi (Mangifera casturi)

Mangwaron Kalimantan (Mangifera casturi) wanda a gargajiyance aka fi sani da Kasturi bishiya ce da ake samu a wurare ‘yan qalilan mai tsawon kimanin mita 10–30 mai fita a qasashe masu zafi a zagayen Banjarmasin a kudancin Borneo (Indonisiya). A halin yanzu babu bishiyar a daji sabo da haramtattun masu saran bishiya. To amma, a wasu lokutan ana noma ta a waxannan wurare sabo da ‘ya’yanta da ke da daxi.

Girman xan itacen Mangwaron Kalimantan (Mangifera casturi) qarimi ne idan aka kwatanta shi da sauran ire-iren mangwaro. Nauyin ko wane xaya yakan kai giram 50 zuwa 84. Idan bai nuna ba, launin xan itacen kore ne – to amma idan ya nuna, sai launinsa ya zama ruwan qasa-qasa ko rawaya kuma yana sheqi, wani lokaci kamar ruwan hoda. Wannan launi yana daga cikin masu ban sha’awa na dangin M. Casturi. Akwai ire-ire guda 3 na Mangifera casturi – Kasturi, Mangga Cuban da Pelipisan. Wanda yafi shuhura shi ne Kasturi sabo da yanayin qanshinsa. Wani lokaci akan xauki Mangga Cuban da Pelipisan a matsayin ire-ire masu zaman kansu. To amma Pelipisan akan same shi da qanshi kuma mai daxi kamar Kasturi, wannan yana nuna cewa wannan xan itace gamin-gambiza ne na Kasturi. Ana buqatar bincike domin tabbatar da gaskiyar wannan lamari.

picture

Xan itacen Mangwaron Kalimantan (Mangifera casturi), Borneo, Indonisiya

Tsokar xan itacen ta yi kama da ta lemon zaqi sannan tana da tauri da kuma daxin qanshi. Idan muka kwatanta Kasturi da Mangwaro (Mangifera indica), Kasturi ba shi da zaqi sosai to amma yana da qanshi mai qarfi kuma mai daxi. Sannan tsokar Kasturi ta fi yawa.

picture

Cikakken bayanin xan itacen Mangwaron Kalimantan (Mangifera casturi), Borneo, Indonisiya

Kasturi sananne ne a cikin mutanen Kudancin Borneo da kuma maqwabtan garuruwa. Qanshinsa na da matuqar daxi har ta kai mutane na yi masa wani tsohon kirari kamar haka: “Seharum kasturi, seindah pelangi, semuanya bermula.” Ma’ana: “Wai Wai Wai, qanshi kamar Kasturi, Kyau kamar bakan gizo. Yanzu na fara wannan qauna”.

Haramtattun ayyuka na saran itace ya haddasa vacewar wannan bishiya a daji. Tsofaffin bishiyoyin Mangwaron Kalimantan na fuskantar barazanar vacewa sabo da ayyukan masu saran itace domin darajar itacenta.Mutane na shuka bishiyoyi kaxan a bayan gidajensu ko a qananan gonakinsu.

Ba kamar sauran bishiyoyin da ke fita a qasashe masu zafi ba, ba’a shuka Mangwaron Kalimantan a manyan gonaki a Indonisiya sabo da rashin hanzari wajen fitowarta Ana iya samun manyan gonakin Mangwaron Kalimantan a shiyyar Mataraman a gundumar Banjar (gundumar Banjar ba xaya take da gundumar Banjarmas ba). Mutanen Mataraman sun yi qoqarin shuka a wata qaramar gona a shekara ta 1980 ta yadda za’a fara girbi a shekarar 2005. Duk da cewa ana samun xan itacen, har yanzu bai wadaci jama’a ba.

Anfanin bishiyoyin Mangwaron Kalimantan ya taqaita ne kawai akan ‘ya’ya da kuma itace. Duk da cewa tsohuwar bishiya na iya samun girman gangar jikin da ta kai mita xaya, mutanen Banjar (mutanen da ke kusa da gavar kogi da kuma cikin qasa a Kudancin Borneo), na amfani da ‘ya’yan sabo da tsawon lokacin da bishiyar ke xauka kafin ta fito. Sabo da wannan dalili, matanen Banjar suke amfani da itacen wasu bishiyoyi masu inganci. Domin samun xan itacen, ba abu ne mai sauqi ba sabo da bishiyar Kasturi na da tsawo ta yadda sai mutum ya hau can sama kafin ya tsinko shi – ‘ya’ya kaxan ne masu faxowa qasa.

Ana iya cin xan itacen xanye ko kuma a matsayin ruwan Kasturi. To amma ba safai akan kai kasuwa domin sayarwa ba, sabo da manoma kanyi amfanida shi a gida. Wasu kayan shaye-shayen da akan yi su ne maxi, alewa, ruwa ko biskit (biskit na gargajiya). To amma waxannan abubuwa na da wahalar samu sabo da a kullum a cikin neman xan itacen mutane su ke domin mutanen Banjar na son sa. Kuma xan itacen na da tsada to amma a wajan mutanen Bajar kwalliya ta biya kuxin sabulu sabo da xanxanonsa mai ban mamaki!

««« Batun baya: Mangwarorin Indonisiya Batun gaba: Noman Mangwaro daga tsaba »»»

Lahadi 24.12.2023 07:32 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare

Dangane da KPR

Logo of KPR - Qungiyar Manoman Lambu ta Slovakiya
KPR - Qungiyar manoman lambu qungiya ce ta qasa-da-qasa. Qara karatu...
Yi musayar ra'ayinka dangane da noman shuke-shuke. Rubuta batu akan lambu, shuke-shuke, noman shuke-shuke da sauransu kuma ka buga shi a yarenka a mujallarmu ta Botanix! Ka tuntuvemu domin qarin bayani.

Category: Duk Bado Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya Ciyawa Dokoki akan noman shuke-shuke Kwakwa Qwari Shuke-shuken qasashen qetare Shuke-shuken ruwa