Botanix – Mujalla akan shuke-shuke

Botanix Hausa

Ta yaya za ka nome lambunka dai dai?

Ya zama wajibi ka san yadda za ka nome lambunka dai dai domin samun ciyawa mai kyau. Babu bishiya mai yanayin qwai da zata yi kyau idan lambu ba shi da kyau!

Kafin noman lambu, sai an lura da qaxannan dokoki – a yanke ciyawa zuwa 1/3. Wannan na nufin cewa ciyawa mai tsawon santimita 6 a rage ta zuwa santimita 4. Tsawo mafi dacewa da ciyawa shi ne santimita 2 zuwa 3. Idan aka rage ta sosai ciyawar na iya mutuwa. Bayan nome ciyawar, sai a bata isasshen ruwa (a qalla daga lita 10–15 a duk 1m ²).

A nan za’a iya amfani da nau’oin noman lambu – hanyar gargajiya da kuma wadda ake kira noman-zamani. Noman lambu ta hanyar zamani baya warwatsa ciyawa, amma yana aske ciyawa ta yi kyau sannan ya ajiye ta a matsayin taki. Ta wannan hanya, lambunka zai sami taki cikin sauqi bayan duk lokacin da aka nome lambu. To amma, wannan hanya bata da inganci idan kana da wajen ninqaya, domin ciyayin na iya shiga cikin ruwan. A nan ya fi kyau ayi amfani da hanya ta gargajiya ta hanyar sa akwati wanda zai tattara duk ciyawar da aka nome.

Akwai kuma inda ake haxa hanyoyin noman guda biyu ta yadda za ka zavi yin amfani da akwati ko kuma a’a.

Wannan ya fi dacewa da lambu mai gangarar 15°. Idan lambunka yana wuri mai tudu, zai yi kyau ka yi amfani da manomi na hannu wanda akan yi amfani da shi a wurare masu wahala kamar qananan wurare ko kusa da bishiya ko gefen furanni.

««« Batun baya: Shuke sabon shinge Batun gaba: Yaya za kayi da nomammiyar ciyawa? »»»

Asabar 23.12.2023 19:07 | buga | Ciyawa

Dangane da KPR

Logo of KPR - Qungiyar Manoman Lambu ta Slovakiya
KPR - Qungiyar manoman lambu qungiya ce ta qasa-da-qasa. Qara karatu...
Yi musayar ra'ayinka dangane da noman shuke-shuke. Rubuta batu akan lambu, shuke-shuke, noman shuke-shuke da sauransu kuma ka buga shi a yarenka a mujallarmu ta Botanix! Ka tuntuvemu domin qarin bayani.

Category: Duk Bado Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya Ciyawa Dokoki akan noman shuke-shuke Kwakwa Qwari Shuke-shuken qasashen qetare Shuke-shuken ruwa