Yaya za kayi da nomammiyar ciyawa?
Idan kana buqatar kyakkyawa, ciyawar da aka aske, sai akai-akai kana nome shingenka. Saurara kaxan, ciyawar da aka nome kan bayar da ciyawa mai yawa wanda wannan matsala ne gareka. Mafi yawan manoman da na sani kan yi maganin ciyawarsu daga sharar gidansu. Sai kawai in girgiza kaina cikin mamakin yadda ake asarar taki mai sauqi!
Ciyawa na yin amfani mai yawa, wanda takin gargajiya xaya ne daga cikin masu mahimmanci (wannan ya haxa da ciyawa, qanzo, busassun qirare da sauransu) kuma ana amfani da su wajen zubawa shuka da fulawowi. Wannan takin gargajiya na taqaita asarar ruwa, yasa qasa ta kasance a cikin danshi kuma ya samar da wani yanayi mai kyau ga qwayoyin halitta. Ciyawar da aka nome wadda muke rufe shuke-shuke, na bayar da abincin da shuka ke buqata.
Wannan takin gargajiya na kare fashewar tumatir da yalo sosai. Idan ka yi amfani da ciyawa a matsyin takin gargajiya zai kare ‘ya’yan inibi, da na vaure daga zubewa a lokacin bazara – kamar dai a wannan shekarar ga misali. Busasshen gangar jikin bishiya wanda sai dai ayi amfani da shi wajen kare wajen shaqatawa ko lambuna bai kai amfanin takin gargajiya ba.
««« Batun baya: Ta yaya za ka nome lambunka dai dai? Batun gaba: Kiwano (Cucumis metuliferus) »»»
Dangane da KPR
Yi musayar ra'ayinka dangane da noman shuke-shuke. Rubuta batu akan lambu, shuke-shuke, noman shuke-shuke da sauransu kuma ka buga shi a yarenka a mujallarmu ta Botanix! Ka tuntuvemu domin qarin bayani.
Category: Duk Bado Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya Ciyawa Dokoki akan noman shuke-shuke Kwakwa Qwari Shuke-shuken qasashen qetare Shuke-shuken ruwa