Kiwano (Cucumis metuliferus)
Kiwano xan itace mai kama da lemon zaqi na da tsawon santimita 10–15. Yana cikin dangin gurji. ‘Ya’yan itatuwan na da zankwaye a vawonsu yadda zai tunawa mutum yanayin kayan yaqi irin na mutanen da. Tsakiyar xan itacen kore ne kuma na da ‘ya’ya a cikinsa masu tsawon milimita 5–10. Lokacin da bai nuna ba xan icen kore ne.
Ana fitar da wannan xan itace daga Isra’ila da kuma Tsakiyar Amurka. Ana cin xan itacen tare da ‘ya’yan cikinsa. Xanxanon kiwano kamar na gurji ne, ko ayaba. Bayan cin kiwano, ana yin anfani da kwanson a matsayin kyawawan farantai; yayinda za a iya shuka irin. Kiwano shuka ce mai saurin fitowa kuma mai yaxo kamar gurji. Ganyenta ya yi kama sosai da na gurji kuma tana da jiki mai laushi.
Yanayin barbarar furen wannan shuka mai tsawon milimita 3 kamar na gurji ne. Mu sani cewa xan itacen wannan shuka na iya ruvewa idan yana ajiye a qasa. Kiwano na iya fitowa a wuri mai zafin da ya kai kimanin 25 ºC, sabo da haka yanayin zafin da ake da buqata a cikin akwatin noma wannan shuka kamar na gurji ne ko kuma kankana. Kiwano ba ta jure rava. Idan kana zaune a wurin da ke da hunturu ko rava, ya zama wajibi ka shuka kiwano bayan wannan yanayi ya wuce.
««« Batun baya: Yaya za kayi da nomammiyar ciyawa? Batun gaba: Cherimoya (Annona cherimola) »»»
Asabar 23.12.2023 19:20 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare
Dangane da KPR
Yi musayar ra'ayinka dangane da noman shuke-shuke. Rubuta batu akan lambu, shuke-shuke, noman shuke-shuke da sauransu kuma ka buga shi a yarenka a mujallarmu ta Botanix! Ka tuntuvemu domin qarin bayani.
Category: Duk Bado Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya Ciyawa Dokoki akan noman shuke-shuke Kwakwa Qwari Shuke-shuken qasashen qetare Shuke-shuken ruwa