Botanix – Mujalla akan shuke-shuke

Botanix Hausa

Cherimoya (Annona cherimola)

Abin sha’awa a halin yanzu ana shigo da kayayyakin marmari na qasashe masu zafi zuwa Turai. Na sami nasarar sayen xan itacen cherimoya kuma na xanxana shi. Ba’a samun sa a shaguna to amma godiya ga xanxanawar da nayi, nan gaba za’a sami wannan xan itace a shago!

Cherimoya shi ne game-garin suna na xan itacen Annona cherimola wanda ake nomawa a tsaunukan Andes daga Kwalambiya zuwa Peru a da’ira mai mita 700–2400. Wannan iri na jure yanayin sanyi kuma ana iya noma shi a wasu vangarori na duniya masu zafi – har ma a Isra’ila da Kudancin Ispaniya. A iya wannan iri mun gano nau’oi a qalla 120.

Jikin bishiyar Cherimoya tsanwa ne mai sirkin baqi-baqi kuma yana da wani irin kama mai ban mamaki kamar wani ya bar zanen hannunsa a jikinta. Za’a iya ajiye koren ‘ya’yan itatuwa a xaki. Xan itacen na da tsoka, kuma da launin madara-madara da kuma xanxano kamar na ayaba kuma/ko abarba. A cikin ko wane kwanso akwai tsaba ja mai kama da wake kimanin 10–20. Akan ci ‘ya’yan xanye.

Za ka iya shuka tsabar a gidanka ko a xaki na musamman. Yanayin fitowarta yana bambanta, to amma mafi yawan lokaci na fita a mako xaya ko uku. Yanayin zafin da take buqata wajen fitowa shi ne kimanin santi 27 °C. Qaramar shukar na kama da fure, to amma ta kan canja cikin lokaci kaxan zuwa tsanwa mai duhu-duhu da kuma ganye yanayin qwai da ko wane na iya kaiwa tsawon santi-mita 10–15 da kuma wasu dogwayen ganyayyaki a bayansu.

A lokacin hunturu, shukar kan kaxar da ganyenta kuma idan aka yi mata rauni tana fidda wani wari na musamman. Sabon reshe na fitowa a gurbin da ganye ya faxi. Duk yanayin shukar annona na buqatar haske da kuma hanya ta musamman ta rayuwa – wannan ya zama wani batun tattaunawa tsakanin manoma! Ni da kaina na shuka annona a fili mai zafin santi 10–15 ºC domin ta fito. A lokacin hunturu manomi na buqatar lura da yadda yanayin fitowar zai kasance dangane da shukar da aka raina a yanayi daban-daban domin ganin wacce za ta fara fita.

Annona na fita sau uku zuwa sau biyar a shekara. Kafin ta nuna annona na yin yaushi sannan ta kaxar da kusan duk ganyenta. Furenta nau’in xorawa ne kuma yana nuna a inda ganye ya faxi ko kuma ya nuna a lokacin da sabon ganye ke fitowa. Wajen barbara ana buqatar shuka guda biyu kuma nunar ‘ya’yanta ya kan xauki kimanin watanni 5–7.

Ka da ka damu da saman shukar da kusan ko yaushe yake yanqwane. Gajeren lokacin rashin ruwa baya cutar shukar, to amma tana buqatar ruwa lokacin hunturu. Idan ka yi sa’a sosai, za ka iya sayen waxannan ire-iren:

Annona squamosa – ferarriyar annona mai kama da ferarriyar abarba. Ana kiran waxannan da tuffa ma zaqi kuma ‘ya’yanta yanayin xorawa ne mai sirki da kore.

Annona muricata – wannan annonar tana da ‘ya’ya masu fita a jikinta kuma manya ne masu nauyin (kilogiram 1,5–5) – suna da rami a jikinsu wanda ya kai zurfin santimita 0,5. Tsanwa ne. Ganyen shayin da ake kira Corosol ana yin sa ne daga ganyen wannan shukar.

««« Batun baya: Kiwano (Cucumis metuliferus) Batun gaba: Noman ciyawar kifi (Pleurotus ostreatus) »»»

Asabar 23.12.2023 19:30 | buga | Shuke-shuken qasashen qetare

Dangane da KPR

Logo of KPR - Qungiyar Manoman Lambu ta Slovakiya
KPR - Qungiyar manoman lambu qungiya ce ta qasa-da-qasa. Qara karatu...
Yi musayar ra'ayinka dangane da noman shuke-shuke. Rubuta batu akan lambu, shuke-shuke, noman shuke-shuke da sauransu kuma ka buga shi a yarenka a mujallarmu ta Botanix! Ka tuntuvemu domin qarin bayani.

Category: Duk Bado Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya Ciyawa Dokoki akan noman shuke-shuke Kwakwa Qwari Shuke-shuken qasashen qetare Shuke-shuken ruwa