Botanix – Mujalla akan shuke-shuke

Botanix Hausa

Noman ciyawar kifi (Pleurotus ostreatus)

Ciyawar kifi (Pleurotus ostreatus) sananniya ce a ‘yan kwanakinnan fiye da ciyawa game-gari (ciyawar champignon)! Dangantaka da ciyawa game-gari, Ciyawar kifi ta na da wata rana guda xaya – ba ta rikicewa da ciyawa mai guba “hular mutuwa” (Amanita phalloides).

Ciyawar kifi (Pleurotus ostreatus) na qunshe da sinadaran gina jiki, sinadarin amino da qarfe, waxanda ke kare jiki daga duk wata matsala ta guba. Kuma ta na rage illar kitse a cikin jini kuma ta na da mahimmanci wajen haxa abinci sabo da qarancin sinadarin calorie da ya ke cikinta. Kuma anyi imani cewa ta na da sinadaran hana kamuwa da cutar kansa.

Qa’idojin shuka ciyawar kifi (Pleurotus ostreatus)

Za’a iya shuka ciyawar kifi ta hanyoyi guda biyu – shukata a kan ciyawa a jakar leda, ko a kan gungumen ice.

Shuka a kan ciyawa a jakankunan lega

A fara shirya ciyawar da farko. Sai an wanke ta da ruwan magani domin kawar da qwayoyin cuta, gansa-kuka da funfuna. Za’a iya wankewa ta hanyoyi biyu:

  1. Ka saka ciyawar a babbar tukunya (buta ko tsohon kasko) sannan ka zuba ruwa ya sha kan ciyawar. Ka dafa shi har zuwa awa xaya a zafin da ya kai 100 °C. Sai ka bari ya huce zuwa zafin 20–25°C.
  2. Na biyu (kuma mafi sauqin) hanya it ace: Zuba ciyawa a babbar tukunya sannan ka zuba tafasasshen ruwa a kanta. Yi amfani da ita idan ciyawar ta yi sanyi zuwa 20–25°C.

Yanzu zuba ciyawar da tattaka a babbar jakar leda – shiryayyar ciyawa, shiyayyar tattaka, shiryayyar ciyawa, shiyayyar tattaka – da sauransu. Jaka guda ta tattaka ta ishi jiqaqqiyar ciyawa mai nauyin kilogiram 15–20 (wannan zai shiga jaka mai santimita 50×100). Idan jakar ta cika, xaure ta sannan ka yi hudoji masu a taqaice santimita 3–5 ko wace a jikin jakar.

Idan ka shuka ciyawar kifi a wuri mai sauqin gumi, za ka iya yin hudoji kaxan (daga baya za ka iya qara wasu idan da buqata) domin kaucewa bushewar ciyawar. Bayan shuka, ka ajiye jakankunan a wuri mai rangwamen rana ta yadda rana ba zata daketa kai tsaye ba.

Yanayi mafi dacewa na noman ciyawar kifi shi ne 15–25 °C. Idan yanayin ya na da ximi, ciyawar kifi ta fi girma sosai. (Duk da cewa tsananin zafi kan busar da ciyawa da sauri.)

Sabo da wannan dalili zai fi kyau a lura da yanayin ximi wanda ciyawar kifi ta fi buqata. Idan funfuna mai yawa ta fito a jikin ciyawar kifi a cikin wani lokaci, sai a ajiye ta a wuri mai sanyi. Idan ka buqaci qarin funfuna, sai ka ajiye ta a wuri mai zafi! Bayan watanni 3 zuwa 4, a lokacin takin da ke cikin jaka ya ragu domin tuni ciyawar kifi ta yi amfani da shi to sai ka sake mata wani tanadi (za ka yi wannan ta sake tattara tsohuwar ciyawa) Jaka xaya za ta baka kimanin kilogiram 2–4 na ciyawar kifi.

Noma akan gungumen ice

A daji, ciyawar kifi kan fito a jikin bishiyoyi masu ganye da yawa. Da wannan dalili, za ka iya nomansu a gungumen ice mai santimita 30–80. Za ka iya amfani da ice na bishiya mai ganyaye (banda bishiya mai yanayin qwai!). Icen kada ya wuce wata 6 da sarowa. Akwai hanyoyi da dama na noman ciyawar kifi a jikin ice. Zai fi kyau idan ciyawar kifi ta fito kai tsaye a jikin icen ta yadda funfunar jikin icen za ta tsiro. Zuba saiwar mycelium a 1/3 na qasar lambunka a wuri mai inuwa. Sabo da bushewa, ka jiqa da ruwa. Saiwar za ta yi ciyawa a shekaru 2–5 masu zuwa (ya danganta da ingancin saiwar).

Sayarda mycelium na ciyawar kifi

««« Batun baya: Cherimoya (Annona cherimola) Batun gaba: NOVODOR FC domin yaqi da qwarin dankalin Kwalarado »»»

Asabar 23.12.2023 19:42 | buga | Bado

Dangane da KPR

Logo of KPR - Qungiyar Manoman Lambu ta Slovakiya
KPR - Qungiyar manoman lambu qungiya ce ta qasa-da-qasa. Qara karatu...
Yi musayar ra'ayinka dangane da noman shuke-shuke. Rubuta batu akan lambu, shuke-shuke, noman shuke-shuke da sauransu kuma ka buga shi a yarenka a mujallarmu ta Botanix! Ka tuntuvemu domin qarin bayani.

Category: Duk Bado Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya Ciyawa Dokoki akan noman shuke-shuke Kwakwa Qwari Shuke-shuken qasashen qetare Shuke-shuken ruwa