NOVODOR FC domin yaqi da qwarin dankalin Kwalarado
Ba na zato sai na gabatar da qwaron dankalin Kwalarado (Leptinotarsa decemlineata) domin kowa ya san wannan babban qwaro mai lalata dankali kuma wanda yake da wahalar kashewa ba tare da sinadarai ba. A wani lokaci, babu wanda ya san yadda za’a yi maganin wannan qwaro na dankalin Kwalarado.
Daga ina ya zo?
Qwaron dankalin Kwalarado ya zo daga Arewacin Amurka zuwa Turai. A wancan wuri yana rayuwa a wasu wurare qalilin a shiyyar Cordillera a inda yake cin ganyayyakin dankali mai fitowa a daji. A lokacin da mutane suka fara noman wannan dankali (sunan turanci: Solanum tuberosum) mai yawan gaske a Amurka, qwaron dankalin Kwalarado sai ya dawo kan dankalin da ake nomawa daga dankalin da ke fita a daji. Godiya ga wannan dankali qwaron dankalin Kwalarado ya yaxa kansa a duniya.
NOVODOR FC – Tarkon qarni na uku?
Novodor FC ya haxa da 2% na sinadarin protin daga halittun Bacillus thuringiensis ssp. tenebroinis. Wannan halitta na da qarfin hallaka tsutsa daga dangin Galerucinae ( mai lalata bishiya kamar bishiyar ash, bishiyar alda da kuma willow) da kuma qwaron dankalin Kwalarado.
Wannan magani na haddasa rashin lafiya ga tsutsar da muka ambata. Bayan ta ci ganyen shukar da aka yiwa feshi, sai tsutsar ta kasa cin komai sannan bayan kwanaki 2–5 sai ta mutu. Ga sauran tsutsotsi wannan ba shi da guba, bai haddasa wata illa ta din-din-din, ga ganyen ko kuma qasar kanta. Tsutsar ce kawai ke hallaka daga wannan magani a lokacin da take jaririya kafin ta girma. Za’ayi amfani da ita ne kawai lokacin da tsutsar take qarama.
Domin gane ingancin wannan magani, ya zama wajiba tsutsar ta ci ganyen da yawa – sabo da haka yake da mahimmanci a yi feshin a sama da kuma qasa ganyen sosai. Ya fi kyau a yi wannan feshi a lokacin da babu iska sosai kuma yanayin ximi ya kasance sama da 15 °C. Idan aka yi ruwa a cikin awa 12 bayan feshin, to sai an maimaita yin feshin.
Ana saida wannan magani a qananan mazubi, a qaramar kwalaba mai milimita 100 kuma farashinta yana kaiwa kimanin Yuro 3 kawai.
Wasu nau’in na wannan halitta kan lalata tsutsar da ke zama Malam-buxa-mana-littafi (Pieris brassicae) da Codling Moth (Cydia pomonella) (substance Biobit FC) da sauro.
A qarshe labari mai daxi: za’a iya cin xan itacen da zaran an gama feshin!
««« Batun baya: Noman ciyawar kifi (Pleurotus ostreatus) Batun gaba: Yaya za ka yi maganin qwaron wake? »»»
Dangane da KPR
Yi musayar ra'ayinka dangane da noman shuke-shuke. Rubuta batu akan lambu, shuke-shuke, noman shuke-shuke da sauransu kuma ka buga shi a yarenka a mujallarmu ta Botanix! Ka tuntuvemu domin qarin bayani.
Category: Duk Bado Bishiya mai bada ‘ya’ya yanayin kaxanya Ciyawa Dokoki akan noman shuke-shuke Kwakwa Qwari Shuke-shuken qasashen qetare Shuke-shuken ruwa