Bishiyar Khasi Pine (Pinus kesiya)

Bishiyar Khasi Pine (Pinus kesiya) iri ne mai saurin fitowa daga Asiya, wadda ba’a nomata a wani wuri daban. Bishiyarta kan kai tsawon kimanin mita 30–35 da kuma kaurin gangar jiki mai murabba’in mita 1. Ko wane reshe na da vangarori uku – ko wane xaya kimanin tsawon santimita 15 zuwa 20. ‘Ya’yan itacen wannan bishiya (cones) suna kaiwa tsawon kimanin santimita 5 zuwa 9 kuma tsawon tsabar ya kai kimanin santimita 1,5 zuwa 2,5.

Asalin bishiyar Khasi Pine (Pinus kesiya) daga shiyyar Himalaya ne: daga Arewa-maso-Gabacin Hindiya (a halin yanzu sabo da saran katako sai a Khasi Mt. da Naga Mt. a jihar Meghalay da Manipur), Sin (shiyyar Yunnan), Bama (Myanmar), Arewacin Tailan, Laos, Vietnam (Lai Chau, Lang Son, Cao Bang, Quang Ninh) da Philippines (Luzon). Wani lokaci akan xauki bishiyar Pine daga Philippines a matsayin iri daban mai suna Pinus insularis. A qasar Sin mutun na iya samun iri mai kama da wannan wanda ake kira Pine xin Yunnan (Pinus yunnanensis)

Ana samun wannan iri a magangara mai mabanbantan bishiyoyi a qasa marar inganci (mai pH na 4,5) da kuma tsawon sama da kogi na mita 800–2000 to amma yawanci yana kaiwa mita 1200–1400. Wurin yana da matsakaicin sanyi da sauye-sauyen yanayi na damina da bazara a cikin shekara. Akan sami ruwan sama mai yawa da shuke-shuke masu yawa da kuma yanayin damina da bazara a cikin shekara tare ruwan sama mai yawa da kuma gumi mai yawan 70%.

Wannan shuka na da sauqin jure rava, to amma ba ta jure rava mai yawa lokacin kaka. A lokacin girbi, tana buqatar wurin da babu rava.

Wasu sunayen wannan shuka su ne: Pinus khasya, Pinus khasyanus

Printed from neznama adresa