Tsabar ganyen shayi
Kafin qarshen hunturu ya qarato, duk manomin lambu yana tunanin mai zai noma a kaka mai zuwa. Zai fi sauqi a noma tumatir, yaji, ko kuma gurji? Ko kuma kana buqatar wani abu? Wani abu daga qasashen waje? Me kake gani game da noman ganyen shayi a bana?!
Shukar ganyen shayi ta (Camellia) na da ire-ire sama da 50 na shuke-shuken qasashe masu zafi da ciyayin wurare masu yanayin zafi ko qananan bishiyoyi waxanda aka fi sani da Ganyen shayin Sin (Camellia sinensis). Wannan daxaxxiyar shuka ta samo asali ne daga Kudunci da kuma Kudu maso Gabas na Sin da kuma Qasashen da suka yi hannun-riga – Hindiya, Bama, Vietnam da Lawos, a inda ake noman wannan shuka qarnoni da dama. Ko da yake ana noma wannan shuka a duk qasashe masu zafi, waxanda suka fi samar da wannan shuka su ne Sin, Hindiya, Sri Lanka da Japan.
Rainon ganyen shayin ka ba abu ne mai wahala ba. Abu mai mahimmanci a wannan lamari shi ne sayen sabuwar tsaba, sabo da tsabar ganyen shayi na rasa ingancinta cikin qanqanin lokaci. Tsabar da’ira ne da ita. Kafin ka shuka ta sai ka jiqa ta tayi kimanin kwanaki 2 zuwa 3. Bayan wannan, sai a shuka ta a qasa wadda aka tace kuma aka cakuxata da ruwa da taki. A yanayin zafin da ke tsakanin santi 20–25 º, tsabar za ta fito a cikin sati 2–4. Idan aka shuka ta a wuri mai rana, qaramar shukar kan girma cikin sauri kuma ana iya cire ta a cikin watanni shida kawai. Godiya ga sabuwar hanyar cira, mutum na iya qirqirar malafarsa ta aiki kuma ya sami kayansa na aiki na rainon bishiyarsa.
A qasashe masu zafi za’a iya noman ganyen shayi a lambu, to amma a wuraren da rava ke sauka sai dai a noma shi a xaki na musamman. Yanayin bazara shi ne lokacin da yafi dacewa da noman ganyen shayi, sannan ana buqatar isasshen ruwa – waxannan yanayi yasa suke bunqasa a qasashensu na asali.
Idan ba a qasashe masu zafi ka ke zaune ba, ganyen shayin da ka ke nomawa a lambunka ko a bayan gidanka ba lallai ne ya sami ingancin ganyen shayin da ake nomawa a qasashe masu zafi ba, za ka sami gamsuwa da nutsuwa idan shukar da ka ke nomawa ta samar maka da fararen furanni.
Idan kana zaune a qasashen da rava ke sauka, lokacin hunturu, ka ajiye shukar ganyen shayinka a kusa da taga. Sabo da shukar ganyen shayi na buqatar ko yaushe ta zama tsanwa kuma mai yiwuwa a lokacin hunturu ta rasa isasshen hasken rana, zata iya yin yaushi kuma ta kaxar da wasu ganyayyakinta. To amma, idan bazara ta kawo kai zata iya farfaxowa ta yadda za ka iya sake cirar ganyenta!
Printed from neznama adresa