Lotun xin Hindiya (Nelumbo nucifera)

picture

Fulawar Lotus xin Hindiya

Lotus xin Hindiya (Nelumbo nucifera) bishiyar ruwa ce mai kyau ganyenta kore ne wanda yakan taso akan ruwa. Fulawarta mai ruwan hoda ana samunta a jikin reshe ta xago santimita da yawa a saman ruwa.

Ana xaukar Fulawar Lotus xin Hindiya da matuqar girmamawa musamman lokacin bukunkuna ga mabiya addinin Buda. Shukar ta dace da ci a wajen xan adam; duk da cewa ana amfani da tsabar da kuma saiwarta a wajen shirya abincin gargajiya a baki xayan Gabas maso Kudancin Asiya. Ana noma Lotus xin Hindiya kamar yadda ake shuka bado. Babu wahala wajen noma wannan shuka a yanayinmu; sai dai kawai mutum ya san yaya ake yi!

Idan mutum zai shuka Lotus xin Hindiya, lallai ne xaye fatar tsabar kaxan (a goge ko asa yashi) da sanfefa. Wannan zai baiwa ruwa damar shiga cikin sauqi, wanda in babu ruwa irin ba zai tsiro ba. Idan aka bar fatar mai qarfi a jikin irin, tsabar za ta iya xaukar qarnoni ba tare da canjawa ba. To amma, idan aka jefa ta a ruwa, za ta iya xaukar shekaru kafin irin ya fito.

picture

Tsiron Lotus xin Hindiya

Ta yaya za ka sani ko ka cire isasshiyar fata mai qarfi ta wannan tsaba?

Mutum zai iya ganewa daga girman tsiron idan an saka shi a ruwa. Idan tsabar ta qaru kamar sau biyu daga girmanta kafin shukar ta cika awa 24, ba’a buqatar sake cirewa. Idan ba haka ba, kana buqatar sake cire fatar, ka sake mayar da ita a ruwa har zuwa awa 24 masu zuwa, sannan ka sake duba girmanta. Za’a yi ta maimaita haka har sai tsabar ta ninka girmanta.

Tsabar na buqatar ruwa ne kawai…

Da zaran an sami nasara wajen cire fatar, a jiqa tsabar a mazubin da aka cika shi da ruwa. Adadin ximin ruwan da ake buqata wajen tsiro ya kasance tsakanin 27°C da 28°C (duk da cewa tsabar kan ninka a girmanta a ximin da ya kai 20°C kawai). A wannan yanayin ximin, tsabar na iya tsirowa da sauri kuma cikin mako xaya zai fara tsiro.

Da zaran ganyen farko ya fara fita, shuka tsabar ko dai a wuri mai tavo ko kuma a mazubin kiwon kifi wanda aka cika shi da ruwa da qananan tsakuyoyi (mazubin ruwa na kiwon kifi, kududdufi). Yawan ruwan da za’a zuba ya kasance santimita 30 daga qasa zuwa sama. Idan aka yi amfani da mazubin ruwa na kiwon kifi mai qananan tsakuyoyi, Lotus xin Hindiya na iya girma musamman idan aka zuba kifi a ruwan.

A hankali, yayin da shukar ke girma, zata buqaci qarin sarari. Za ka iya shuka ta a kududdufi a lokacin hunturu, lambu, ko kuma duk wani wuri da babu sanyi sosai. Yanayin zafin da ake buqata wajen noman Lotus xin Hindiya shi ne tsakanin 20°C da 35°C.

A irin yanayinmu, yanayin sanyi ya fi yawa to amma shukar na iya rayuwa ba tare da matsala ba. A yanayin bazara za’a iya fitar da shukar waje, ta amma a hunturu sai dai a barta a gida. A lokuta mafiya tsanani, za ta iya rayuwa a yanayin danshi kamar dai yadda bago yake yi.

Hanya mafi dacewa ta noman Lotus xin Hindiya shi ne ta amfani da bututu mai xaukar daga lita 60 ko 80 na ruwa – wannan na iya kaiwa Yuro 10 ko wane xaya. Yin amfani da wannan hanya: Ajiye tsabar da ta fara tsiro a wuri mai tava ko a cikin mazubin ruwa na kiwon kifi, a zuba tsakuyoyi a ciki, ko a tukunyar fulawa. Domin samun kyakkyawan sakamako, a cika su da ruwa.

Dalilin yin amfani da tukunyar fulawa shi ne zaka iya ajiye ta a lambunka ko kuma a gidanka. A can gaba, yafi kyau a ajiye tukunyar kusa da taga (musamman a baranda) domin tabbatar da cewa Lotus xin Hindiya ya sami cikakken hasken rana. A lokacin bazara, za ka iya ajiye tukunyar a vangaren kudu na barandar ko kuma a cikin lambu. Kamar yadda ka ke gani, za ka iya noman Lotus xin Hindiya – ko da a farfajiyar gini!

Printed from neznama adresa