Fragrant Mango (Mangifera odorata)
A tsibirin Borneo na Indonisiya akwai ire-iren Mangwaro 34 (Mangifera) wanda ya ke fitowa a tsibirin. Yawancin waxannan ire-ire na fuskantar barazanar vacewa sabo da gurgusowar hamada. Wasu daga ire-iren Mangwaron, misali Mangwaron Kalimantan (Mangifera casturi) tuni ya vace daga daji.
Sauran ire-iren bishiyoyin Mangwro daga Borneo misalin Mangifera griffithi (wanda aka fi sani da waxannan sunaye na gargajiya: asem raba, da romian), Mangifera pajang (asem payang), Mangifera quadrifida (asem kipang) da Mangifera torquenda (asem putaran).
Fragrant Mango (Mangifera odorata) sanannen irin Mangwaro ne da ake nomawa a Kudu-maso-Gabacin Asiya. Gamin gambiza ne tsakaninsa da sauran Mangwarori (Mangifera indica) da Horse Mango (Mangifera foetida). An fi saninsa a gargajiyance da: : kuweni, kuwini (a yaren mutanen Indonisiya); kweni, asam membacang, macang, lekup (a yaren mutanen Malay); kuwini, ambacang, embacang, lakuik (a yaren mutanen Minangkabau); kuweni, kebembem (a yaren mutanen Betawi); kaweni, kawini, bembem (a yaren mutanen Sundan); kaweni, kuweni, kweni (a yaren mutanen Java); kabeni, beni, bine, pao kabine (a yaren mutanen Madurese), kweni, weni (a yaren mutanen Balinese); mangga kuini (a Arewacin Sulawesi); da kuini, guin, koini, kowini, koine, guawe stinki, sitingki, hitingki (a tsibiran Maluku).
Printed from neznama adresa