Noman Mangwaro daga tsaba

Ka shuka sabuwar tsaba domin samun kyakkyawar tsirowa. Ka jiqa tsabar a ruwa mai ximin kimanin 20–25 °C zuwa kimanin awa 2–6.

picture

Wankakken irin Mangwaron Kalimantan, Kasturi (Mangifera casturi), Borneo, Indonesia

Bayan jiqawa, shuka irin a qasa (marar nauyi, mai rairayi) kuma ya kasance ximin tukunyar ya kai a qalla 20–25 °C. Tsaba za ta fito a cikin makwanni 1–3. A ajiye jaririyar shuka a waje mai sauqin zafin rana.

picture

Tsirar tsabar Mangwaron Kalimantan, Kasturi (Mangifera casturi), Borneo, Indonesia

Idan kana zaune a qasashe masu zafi, za ka iya shuka bishiyar Mangwaron a lambunka. Idan kana zaune a qasar da ke da sanyi ko rava, ya zama wajibi ka adana shukar Mangwaron a cikin gida ka kuma a xaki na musamman.

Printed from neznama adresa