Bishiyar Taba (Nicotiana glauca) – bishiyar kan baranda abar hange daga nesa!

picture

Bishiyar Taba (Nicotiana glauca)

Buqatar xan adam ta sabon abu, mai ban mamaki da abin da yake ba-saban-ba taqaitacce ne. Sabo da haka, manoman lambu ke mafarkin wani abu sabo a lambunsu – wani abu wanda ba kowa ya ke da shi ba. Da wannan dalili Kasuwar shuke-shuke ke bawa manoma wani abu sabo a duk shekara – domin kwantar da qishirwar da manoma ke da ita wajen samun abu na asali. Gabatar da sababbin ire-ire zai sanya shukar bishiyar taba ta shiga duk hannun manoma ba da daxewa ba.

picture

Bishiyar Taba (Nicotiana glauca)

Shekaru goma da suka wuce sababbin qirqire-qirqire akan shuka na zuwa ne daga shuka mai bayarda inuwa dangin (Solanaceae). Sanannu daga cikin waxannan su ne petunia, surfinia, da kuma shuka mai matuqar farin jini (Calibrachoa). Sirrin nasararsu na cikin saurin girmansu, saurin yin huda (idan suka fito daga tsaba sukan girma cikin wata uku, idan kuma dasa su aka yi, nan-da-nan su kan girma) kuma da cewa ba su buqatar wani sharaxi wajen girmansu. Sun fi buqatar wuri mai rana, to amma tana fitowa a wuri mai duhu da kuma wuri mai sanyi.

To amma, shuke-shuke dangin shuka mai bayar da inuwa ba sanannu ba ne. Yi tunanin misalin dankali ba tumatir da a wani lokaci ake noma su sabo da kyansu! A lokacin da labari ya zo cewa za’a iya cin wannan shuka, sai mutane suka qi sakin jikinsu. To amma a yanzu ana cinsu a kusan duk qasashen duniya kuma har abincin gargajiya ana saka waxannan shuke-shuke!

picture

A wannan batu za mu gabatar muku da wannan shuka ta bishiyar taba (Nicotiana glauca) – shukar baranda da ba sanniya ba sosai wadda ta samo asali daga Kudancin Amurka. Bishiya ce mai saurin girma. Tana fara fitowa bayan watanni biyu da shuka ta, kuma a cikin wata xaya reshenta na iya kaiwa santimita 50–70.

Kamar dai yadda sunanta na turanci ke nunawa (glauca=kore), shukar tana da nau’in kore mai ruwan gwal. Sabo da haka, ba’a tava ta domin kada ta rasa kyanta na ruwan gwal da wuri kuma ya canja nau’in shukar zuwa marar sha’awa. Ganyenta kuwa ruwan azurfa ne, mai yanayin qwai kuma yana da tsini a qarshensa. A qarshen ko wane reshe akwai qananan resuna masu xauke da fure mai ruwan xorawa kimanin 20–40. Furen na kaiwa tsawon santimita 3–3,5 kuma faxinsa na kaiwa santimita 0,5. A farkon lokacin da furen ke fitowa, yana da nau’in ruwan xorawa mai haske a qarshensa kuma kore-kore. Bayan ya gama fitowa sai nau’in ya zama ruwan xorawa mai duhu. Savanin petunia, furen wannan shuka na daxewa da kamarsa har zuwa wani lokaci mai tsawo.

Noman wannan iri yana da sauqi. Za ka iya shukar bishiyar tabar (Nicotiana glauca) a cikin gidanka ko kuma a waje a lokacin bazara. Za ka iya ninkasu ta hanyar tsabarsu, wadda kan fito da sauri kuma tana da qarfin fitowa. Shukar na fara girma cikin wata biyu (sabo da haka idan kana buqatar barandarka ta yi ado da furanni a watan Mayu sai ka shuka su a watan Maris).

Idan kana zaune a wajen da rava ke sauka, sai ka ajiye bishiyar tabar a wurin da babu rava. Dangane da Pelargonium, za ka iya ajiye waxannan shuke-shuke a wuri mai sanyi (amma mai haske) a lokacin hunturu. A qarshen hunturu, za ka iya rage resunan da rabi kuma ka basu ruwa mai yawa. Shukar taba na iya bunqasa cikin wata xaya. Wannan shuka na iya yin bishiya nan-da-nan, wadda za ka iya ajiyewa a cikin gida. To amma ba’a dashenta domin ba ta yin saiwa da sauri (to amma wannan ba matsala ba ce domin shuka tsabar ta yana da sauqi).

Dangane da amfaninta, shukar taba ba mai neman abubuwa da yawa ba ce. Domin samun fure mai yawa, za ka iya qara mata ruvavvun ganyayyaki da suke aiki a matsayin taki.

Printed from neznama adresa