Yaya za ka yi maganin qwaron wake?

Ina zato ba sai na gabatar maka da qwaron wake ba. Wannan wani qaramin qwaro ne girmansa milimita 3–4, da ake samu a tsaba a cikin xakin girki ga misali.

Wannan maxarnacin qwaro yana haifuwa a duk tsaba mai kwanso. A gaskiyance, duk wata tsaba mai kwanso na da wasu daga cikin wannan halitta – gujiya – qwaron gujiya (qwaro), jinvirin wake – qwaron jinvirin wake, lentils – qwaron lentils, waken lambu – kwaron waken lambu da sauransu.

A jikin lalatacciyar tsaba za ka sami lahani da hudoji waxanda tsutsar ta yi. Idan babban qwaron ya yi qyanqyasa, sai hudojin su bayyana a jikin tsabar. Qwaron wake ya fi varna a lokacin ajiya (sabo da wannan yanayi ya fi dacewa) duk da cewa za’a iya samu cewa tsabar ta gurvata tun daga lambu.

Anyi sa’a cewa yaqi da wannan qwaro yana da sauqi da kuma inganci (yiwuwar nasara 100%!)

picture

Qwaron wake a tsabar Erythrina lysistemon

Da zaran an cire kwanson tun lokacin da ya nuna, vare su sannan ka shanya, kuma ka tabbatar ba bu gurvataccen iri a cikinsu. Ka zubar da duk tsabar da ta gurvata (hanyar da ta fi dacewa ita ce ta qona su). Bayan haka zuba tsabar a roba ko kuma jakar auduga sai ka saka a cikin babban firinji har zuwa awa 48. Ta haka za ka karya matakin girma na qwaron.

Bayan ka fito da tsabar daga babban firinji, sai ka busar da su a cikin xaki har zuwa kimanin kwanaki 2–3. Kana iya barin tsabar a roba har zuwa lokacin da za ka yi amfani da ita. Tsabar da aka adana ta wannan hanya na gurvata ne kawai da tsabar da aka siyo daga shago.

Da wannan dalili, ya fi kyau ka adana tsabar a cikin kwalaba mai mirfi. A tabbatar cewa tsabar ta bushe sarai, idan ba haka ba za ta ruve. Ta wannan hanya kana da tabbaci cewa tsabarka ba za ta gurvata da qwaruka ba.

Kuma za ka iya yaqi da qwaron wake ta zavar tsabar da ta fi dacewa – akwai irirrukan da qwaron wake ba ya so.

Printed from neznama adresa